A ranar Laraba da ta gabata, al’ummar musulmi daga sassan ciki da wajen Jihar Kaduna sun halarci addu’ar kwana 40 ta marigayi Iyan Zazzau Alhaji Muhammadu Bashari Aminu.
Limamai da malamai da dama sun yi addu’o’in neman rahama da gafara ga marigayi Iyan Zazzau Alhaji Muhammadu Buhari Aminu.
A dai lokacin wannan addu’a da aka shafe fiye da sa’o’i uku, wasu malaman da suka yi addu’o’in sun roki rahamar Ubangiji ga marigayi Iyan Zazzau Alhaji Bashari Aminu na ayyukan tallafa wa addinin Musulunci da tallafa wa marasa karfi da suka hada da nakasassu da makarantun Islamiyya da suke sassa daban – daban na Nijeriya ba masarautar Zazzau kawai ba.
Fitaccen malamin addinin musuluncin nan Shekh Malam Mai Nasara Tudun Wa’da, bayan ya gabatar da addu’a ga marigayin,sai kuma ya mika ta’aziyyarsa ga iyalan marigayin da su dauki wannan rashi Iyan Zazzau a matsayin rashi ne na al’umma baki daya musamman bisa irin yadda ya yi amfani da inda damar da Allah ya ba shi wajen tallafa wa al’umma na kusa da na nesa da shi, wannan ya zama wajibi ga ‘ya’yansa, a cewarsa da su you ko yi da shi,wajen aiwatar da ayyukan alherin, kamar yadda marigayin ya yi a tsawon rayuwarsa.
Shi ma wan marigayin Kuma Wannan Zazzau Alhaji Abdulkarim Aminu, ya bayyana. marigayi dan uwansa a matsayin mutum mai ibada da sa da zumunci da girmama na gaba da shi da Kuma duk wani mutum girman da Allah ya ba shi.
A cewar Wamban Zazzau Alhaji Abdulkarim Aminu, babu ko shakka tun daga ‘yan uwanmu da na kusa da nesa da marasa karfi da marayu da dai sauran al’umma,sun an yi asarar shugaban nagari da babu abin da ya sa a gabansa sai tallafa wa al’umma da kuma addini a kowane lokaci..
Wamban Zazzau Alhaji Abdulkarim Aminu ya kammala da bayyana godiyarsa ga al’umma da suka kasance tare da iyalansa domin mika ta’aziyyarsa ga iyalai da kuma ‘yan uwan marigayin.