Al’ummar Rafin Gora Sun Koka Ga Gwamnatin Jihar Katsina

Daga Balarabe Abdullahi, Zariya

Saboda ruwan sama da aka yi kamar da bakin kwarya a karamar hukumar Danja,da ke jihar katsina,al’ummar da suke amfani da hanyayar Rafin gora zuwa Buzaye,sun yi kira tare da kuka ga gwamnan jihar Katsina,AlhajiAminu Bello Masari,da ya duba matsalar rushewar gadar Rafin gora zuwa Buzaye da matsalar ta faru a kwanakin baya.

Mai Magana da yawun al’ummar da aka ambata,Alhaji Yunusa Ali Dan Kaka, Rafin gora ya nuna wannan bukata a ganawar da yay i da wakilinmu a Zariya.

Ya ce, daga kwashe gadar da ruwan sama ya yi a kwanakin baya, al’ummar da aka ambata suka tsinci kansu cikin matsalolin da bas a misultuwa,na rashin gadar da aka bayyana.Ya kara da cewar,kasancewar al’ummar Rafin gora zuwa Buzaye ba su da wata hanyar da suke amfani da ita sai wannan hanyar,sun shiga wani halin matsuwa,kwarai da gaske.

Kan haka,Alhaj Yunusa Dan kaka ya roki gwamnan jihar katsina da kuma shugaban karamar hukumar Danja tare da kansilolinsa,da su dubi matsalar da al’ummar Rafin gora zuwa Buzaye suke ciki,musamman na wannan lokaci na damuna da in al’ummar suka motsa domin fitar da amfanin gonakinsu,ya ce ba karamin matsala za su fuskanta ba

Alhaji Yunusa Ali Dan kaka,ya ci gaba da cewar,al’ummomin garuruwan da aka ambata,suna bayar da gagarumin gudunnuwa a duk lokacin da aka kada kugen zabe,a nan sai ya ce a’ummomon suna fuskantar matsalolin kamfar ribar dimuradiyya.

Da kuma yake tsokaci kan ayyukan ci gaba da gwamnatin jihar Katsina ke aiwatarwa,sai ya jinjina wa gwamna Masari na yadda yake aiwatar da ayyukan ci gaba da gwanatinsa ke aiwatarwa,ya ce yana fatan wadanda ke cikin gwamnati tsundu,da su ci gaba da hadada hada kai da gwamnati,da iya zama silar ci gaban jihar katsin baki daya.

Exit mobile version