Daga Sabo Ahmad
Wani matashin dan siyasa da ke zaune Hayin-dogo, Samarun Zariya, Idris Garba, ya bayyana cewa, amatsayinsa na wanda ya jajirce wajen ganin an zabi jam’iyyara APC a zabukan da suka gabata, kuma jama’a suka amsa kiransu, cike yake da farin ciki a halin yanzu, domin yana alfahari da cewa, al’ummar wannan yanki ba su yi zaben tumun-dare ba.
Idris ya nuna farin cikin nasa ne lokacin yake zayyano aiki da kantoman karamar hukumar Sabon-gari Injiya Muhammad Usman, ya yi musamman wadanda suka taimaka wa ci gaban rayuwar al’ummar wanna yanki.
Ya kara da cewa, Injiniya ya taimaka wa matasa musamman waneman ilimi da koyon sana’o’i, domin samar da hanyoyin dogaro da kai, wanda kuma a halin yanzu kwalliya ta biya kudin sabulu, dominkuwa akwai matsa da yawa da suka gama karatunsu wadansu har sun samu aikin yi wadansu kuma na cigaba da gudanar da sana’oin da suka koya.
Saboda haka, sai Idris ya bukaci al’ummar wannan yanki da ma na kasa baki daya da su tabbatar sun zabi mutanen kirki a zabukan da ake fuskanta nan gaba.