Al’ummar Sabon-gari Sun Yi Dacen Shugabanni -Idris Garba

Daga Sabo Ahmad

Wani matashin dan siyasa da ke zaune  Hayin-dogo, Samarun Zariya, Idris Garba, ya bayyana cewa, amatsayinsa na wanda ya jajirce wajen ganin an zabi jam’iyyara APC a zabukan da suka gabata, kuma jama’a suka amsa kiransu, cike yake da farin ciki a halin yanzu, domin yana alfahari da cewa, al’ummar wannan yanki ba su yi zaben tumun-dare ba.

Idris ya nuna farin cikin nasa ne lokacin yake zayyano aiki da kantoman karamar hukumar Sabon-gari Injiya Muhammad Usman, ya yi musamman wadanda suka taimaka wa ci gaban rayuwar al’ummar wanna yanki.

Ya kara da cewa, Injiniya ya taimaka wa matasa musamman waneman ilimi da koyon sana’o’i, domin samar da hanyoyin dogaro da kai, wanda kuma a halin yanzu kwalliya ta biya kudin sabulu, dominkuwa akwai matsa da yawa da suka gama karatunsu wadansu har sun samu aikin yi wadansu kuma na cigaba da gudanar da sana’oin da suka koya.

Da ya juya kan danmajalisa maiwakiltar wannan yanki na Sabon-garin kuwa, Muktar Isa Hazo, shi ma ya ce, ba kashin yarwa ba ne, domin yana taimakon al’ummar yankin ta hanyar samar da ayyukan raya kasa da ci gaban al’umma’

Saboda haka, sai Idris ya bukaci al’ummar wannan yanki da ma na kasa baki daya da su tabbatar sun zabi mutanen kirki a zabukan da ake fuskanta nan gaba.

Exit mobile version