Al’ummar Soba Sun Roki Sarkin Zazzau Ya Sa Baki Kan Aikin Hanyar Zariya Zuwa Jos

Sarkin Zazzau

Daga ABUBAKAR SADEEK MOHAMMED, ZARIA

 

Shugaban rukunonin kamfanin ASD, Alhaji Sani Dauda ya roki Mai Martaba Sarkin Zazzau Malam Ahmed Nuhu Bamalli da ya sa baki wajen kiran gwamnati ta waiwayi aikin hanyar Zariya Zuwa Jos.

 

Ya yi wannan rokon ne a lokacin  kaddamar da sabon masallacin Juma’a da ya gina a garin Soba, jihar Kaduna, wanda Mai Martaba Sarkin Zazzau, Malam Ahmed Nuhu Bamalli ya bude,ranar Juma’at da ta gabata.

 

Alhaji Sani Dauda ya ce, hanyar tana da matukar mahimmanci, ganin yadda ta ratsa garuruwa da kauyuka masu yawa wadanda dukkansu wurare ne na Noma.

 

Ya ce, kusan tsawon shekara shida ke nan da gwamnatin tarayya karkashin jagorancin Shugaba kasa Muhammadu Buhari ta bayar da aikin wannan hanya, amma har ya zuwa yanzu babu wani abin a zo a gani da aka yi.

 

Saboda haka, sai ya roki Sarki da duk lokacin da ya yi tozali da Shugaban kasa ya sanar da shi halin ha’u la’i da hanyar take ciki.

 

Shugaban rukunonin kamfanonin ASD ya bukaci a gaggauta gina hanyar don rage hadarurruka da ake sama kusan kullum, tare da kara ayyukan ta’addanci da ake gudanarwa sakamakon lalacewar hanyar.

 

Sani Dauda, har ila yau ya koka bisa rashin wata babbar makarantar gaba da sakandire a yankin.

 

“Hakan ba karamin koma baya bane ga yankin musamman ganin yadda garin yake bunkasa, ga kuma dimbin matasa wadanda duk shekara ake yaye su daga makarantu daban-daban na yakin.

 

“Don haka Muna rokon Mai Martaba Sarki da ya taimakawa al’ummar Soba wajen Kai kokon barar mu ga hukumomar ilmi don Samar da wata babbar makaranta don cigaban matasan yankin.” ASD ya ce.

 

A zantawar wakilinmu da Garkuwar daliban Arewa kuma wakilin manoman Arewa, Alhaji Salisu Nuhu Mai masara Soba jim kadan bayan kaddamar da sabon masallacin Juma’ar, ya yi godiya ga Mai Martaba Sarkin Zazzau da ya halarci kaddamarwar da kanshi.

 

Ya Kuma roki Allah ya saka was Alhaji Sani Dauda da alheri bisa kokarin da yake yi wajen ciyar da addinin musulunci gaba.

 

Mai Masara ya kuma roki gwamnatin jihar Kaduna da ta sanya karamar hukumar Soba cikin tsarin ta na inganta karkara domin samar masu da abubuwan more rayuwa

Exit mobile version