Umar A Hunkuyi" />

Al’ummomi A Jihar Kogi Sun Bar Wuraren Zamansu Bayan Da Aka Kai Masu Mummunan Farmaki

Al’ummomin Bagana da na Ogba, da ke karamar hukumar Omala, ta Jihar Kogi, sun watse daga garuruwan na su, tun makwanni uku da wasu ‘yan bindiga da ake kyautata zaton makiyaya Fulani da ‘yan kabilar Agatu ne, suka kai masu mummunan farmaki.
Sa’ilin da wasu mazauna yankin suke dora laifin harin a kan wasu masu dauke da makamai daga kabilar Agatu, da ke makwabtaka da su a Jihar Benuwe, wasu kuma suna zargin Fulani ne da laifin kai farmakin.
A ranar 7 ga watan Afrilu ne, masu dauke da makaman da yawan su ya kai kimanin 300, suka kai farmaki daga al’ummun da suke kusa da bakin kogi a kan iyakan Jihohin Nasarawa da ta Benuwe, suka kashe tare da nakasa mutanen yankin tare da kone gidajen su masu yawa.
An ce sun kashe mutane 8 tare da ‘yan sanda 3, suka kuma jikkata mutane masu yawa, a yanzun haka duk mazauna wajen sun bar garuruwan na su a sabili da farmakin.
Bagana wanda yake da mutane sama da 20,000 a cikin sa, yana karamar hukumar ta Omala ne da ke cikin Jihar ta Kogi, gari ne wanda kabilu masu yawa suke zaune a cikin sa, da suka hada da kabilun Igala, Agatu, Hausa, Nupe, Ebira, Igbo, Kanuri, Fulani da ma wasu da dama, suna kuma zama tare ne a cikin zaman lafiya tun kafin a fara samun sabani a tsakanin Fulani da kabilar Agatu da ke Jihar Benuwe, a shekarar 2013.

Exit mobile version