Al’ummun Australia Kusan Dubu 8 Sun Bukaci A Shigo Da Allurar Rigakafin COVID-19 Daga Sin

Daga CRI Hausa,

Bayanan tashar yanar gizon majalisar wakilan tarayyar Australia sun nuna cewa, a kwanakin baya wasu al’ummun kasar sun gabatar da rokon sa hannu ta kafar yanar gizo, inda suka kira gwamnatin kasar da ta shigo da allurar rigakafin cutar COVID-19 daga kasar Sin tun da wur wuri, domin dakile yaduwar annobar a kasar ta Australia, sakamakon karancin allurar.

An lura cewa, ya zuwa yammacin jiya 4 ga wata da misalin karfe 2 da rabi, gaba daya adadin mutanen da suka sa hannu kan takardar rokon mai lambar EN3158 ya riga ya kai 7979, kuma saura kwanaki 19 suka rage kafin a kammala aikin, dalilai da aka bayyana domin gabatar da takardar rokon sun hada da tsananin yanayin fuskantar yaduwar annobar da kasar ke ciki, da karancin allurar rigakafin, sun kara da cewa, ya zuwa ranar 14 ga watan Agustan da ya gabata, Sinawa sama da miliyan 770 sun riga sun kammala samun allurar, kuma alluran kasar Sin suna da inganci da kuma araha, an riga an samar da su ga al’ummun kasashen duniya, a don haka suna fatan majalisar wakilan Australia za ta yi bayani kan alluran rigakafin kasar Sin, haka kuma za ta shigo da su kasar daga kasar Sin a kan lokaci.(Mai fassarawa: Jamila daga CRI Hausa)

Exit mobile version