Connect with us

RAHOTANNI

Al’umomin Da Guguwa Ta Yi Musu Barna A Bauchi Sun Nemi Agajin Gwamnati

Published

on

Kamar yadda duniya ta sani, irin yadda wata Guguwa ta yi wa jama’an jihar Bauchi mummunar barna a ranar Asabar 16/6/2018 wacce lamarin ya kai ga barnata dukiyoyi, gidaje, massalatai, shagona, kasuwanni da sauran ababen jama’a na dubban miliyoyin naira.
Wasu jama’an jihar Bauchi da ibtila’in ta shafa, suna ci gaba da mika bukatarsu ga gwamnatin tarayya, gwamnatin jihar Bauchi, kungiyoyin agajin gaggawa na kasashen waje da cewar su taimaka wajen kawo wa jama’an jihar Bauchi dauki domin su samu nasarar gyara gidajensu da muhallansu da Guguwar ta yi wa mummunar barna.
Jama’an dai sun bayyana bukatarsu ne a lokacin da ake zagayen duba halin da suke ciki, inda mafiya yawan unguwani suka shaida yadda wannan mummunar Guguwar ta lalata musu muhallai.
Mai Gundunmawar Dan Iya, Alhaji Sulaiman Ahmad Bashir ya shaida cewar a Gudunmawarsa kadai kawo yanzu sun iya tantance kimanin gidaje 180 da Ibtila’in ya shafa, daga cikinsu 40 sun tabbatar dukkaninsu sun rushe a sakamakon wannan Guguwar, wanda hakan ya janyo masu mallakin gidajen kasance basu da wuraren kwana.
Ya ce, “Yanzu haka muna iya ka bakin kokarinmu wajen ganin mun tabbatar da tantance wadanda wannan ibtila’in ya shafa, amma ya zuwa yanzu muna da lissafin gidaje 180 wadanda Guguwar ta barnata, a cikin 180 akwai gidaje 40 wadanda Guguwar ta shafesu gabaki daya ma babu abun da Guguwar ta ragar musu a cikin wannan Gundumawar tawa kadai, Allah kadai ya san na sauran yankuna,” In ji Shi.
Alhaji Sulaiman Bashir wanda ya danganta lamarin a matsayin ibtila’i mai matukar girmar gaske wanda hakan ta sanya ya yi kira ga hukumomin gwamnati, bangarorin gwamnati, hukumomin bayar da agajin gaggawa da kuma masu hanu da shuni da taimaka domin rage wa jama’an Bauchi radadin wannan ibtila’in da ta auku musu.
A nashi bangaren, Mai Gundumawar Dan Amar, Malam Hassan Bayero ya yi kira ga gwamnatoci da su tausaya wa wa jama’an da wannan matsalar ta shafa gami da kuma yin rabon kayyakin da za ta taimaka musu da su bisa adalci, “Ba daidai ba ne, idan aka tashi raba kayyan jinkai a nemo wasu wadanda lamarin bai ma shafa ba; don haka gwamnatoci su tabbatar dukkanin wadanda za su taimakawa wadanda lamarin ta shafa ne kai tsaye,” In ji shi.
Ya bayyana cewar gidaje da dama ne suka gamu da wannan ibtila’in a unguwarsa.
Shi ma dai mai Unguwar Dawaki da ke cikin karamar hukumar ta Bauchi Abubakar Nuhu ya alakanta wannan lamarin a matsayin wata jarabace daga Allahu Subhanahu Watala, inda ya yi kira ga masu sayar da kayyakin gine-gine da su guje wa kara farashin kayyakinsu a sakamakon tsananin bukatar kayyakin da jama’a ke da shi a wannan lokacin.
Dakta Bala Sulaiman Dalhat wanda malamin jami’ar ATBU ne, shi ma ya nemi gwamnatin tarayya da na jahohi da su kawo wa jama’an jihar Bauchi dauki dangane da wannan ibtila’in na guguwa, ya kuma bayyana wannan ibtila’in a matsayin saukakkiya daga Allah, ya shaida cewar kiran ya zama dole ne yadda iskar ta rufafi gidajen dubban mutane a jihar, wanda hakan ya tilasta wa magidanta da dama barin matsugansu izuwa makwafta domin samun mafaka, “Mutane da dama sun bar gidajensu da suka rushe zuwa na makwafta, wasu gidajen sun rushe dukka, wasu kuma sun rasa wasu wajajen,” In ji shi.
Malamin Jami’ar ya kuma bayyana cewar ba daidai ba ne masu sayar da kayyakin gine-gine su kara farashi kan wannan matsalar.
Wani mai suna Isa Jibrin wanda kuma kwamandan ‘yan kwat da gora ne, wanda shi ma guguwar ta auku kan gidansa ya bayyana cewar wannan lamarin ya daukesa daga Allah, don haka ne ya nemi wadanda abun ya shafa da su koma ga Allah, ya bayyana cewar ya wajaba a kan jama’an unguwani da su kare dukiyoyin da suka salwanta a unguwanninsu domin kauce wa masu mummunar zuciya don kada su sace irin su wayan wuta da sauransu.
Wani magidanci wanda gidanta ta kwaranye gabaki daya, ya shaida wa wakilinmu cewa, “Ban san ta ina ne gwamnati za ta fara taimaka wa jama’a ba; amma mafitar kawai shine a taimaka wa jama’a, ni da nake maka Magana, na gamu da wannan ibtila’in, amma ni gaskiya ina da halin da zan yin a gyara nawa koda daki guda ne. abun tambayar shin wadanda basu da ko kudin bulok 100 ya za su yi kenan alhali gidansu ya rushe gaba daya? Wannan lamarin da bukatar gwamnati ta sanya kwamiti mai karfin gaske da zai yi aiki wajen taimaka wa jama’an da wannan ibtila’in ya shafa,” In ji Ahmad Usman daga unguwar Inkil.
Shi kuma Anas Bakaro, wanda shi ma guguwar ta illata masa gida a unguwar Inkil, cewa yake, “Gaskiyar Magana shine kada wani ya tsaya jiran tallafi daga gwamanti ya tashi tsaye kawai ya yi duk abun da zai iya domin gyara dan abun da zai iya gyarawa. Amma wadanda kuma basu da yadda za su yi, muna rokon gwamnati ta tausaya wa jama’anta ta shiga duk inda za ta shiga ta kai wa irin wadannan mutanen tallafi koda da kayyakin gine-gine ne, wannan lamarin ya wuce duk inda kake tunani. Allah ya kare mana gaba,” In ji Anas.
“Halima Shehu Sunana, Ina da zama a unguwar Dawaki, mu bamu da halin gyara gidanmu, a zancen nan da nake yi da kai muna zaune ne a gidan aro, kuma a matukar takure muke, babu yadda za mu, mai gidan bai da kudin da zai iya daga gini gaskiya. Muna neman tallafi a wajen Allah,” A cewarta.
“Maimuna ce sunana, ka dai ga gidanmu da kanka ai ko. To ni bar zan yi magana ne kan yadda irin dumbun asaran da jama’a suka yi na kayyakinsu, kayan gine-gine ba Magana, to a lokacin da ruwan ke barna kayyakin jama’a da daman gaske sun salwanta, wasu kuma sun yi matukar lalacewa,” In ji ta.
“Gaskiya ina jawo hankalin masu saida kayyakin gini irinsu kusa, kayyakin rufi, siminti da bolok da cewar su ji tsoron Allah su daina kara kudi akan kayyakinsu domin wasu jama’an su samu damar gyara gidajensu. Muna rokonsu ne, Malam yau idan ka je sayen kusa sai ka sha mamaki, kusan naira dari yau ya zama dari uku, hatta falange an kara masa kudi, ina za mu yi da rayuwarmu, kudin babu a hanun jama’a ga kuma tsadan kayyaki, muna jawo hankulan jama’a su ji tsoron Allah kada su kara kudaden nan, duk da wasu ma sun rigaya sun kara,” In ji Malam Ashiru Husaini wani magidanci da lamarin ya shafa a lokacin da ke ganawa da wakilinmu.
Wakilinmu ya shaida mana cewar haka zancen yake da mafiya yawan jama’an da abun ya shafa, inda suke matukar kukan rashin babu a hanunsu ga kuma aukuwar wannan ibtila’in, don haka ne ‘yan jihar da daman gaske suka nemi gwamnatin ta tashi tsaye domin kai daukin gaggawa da zai rage musu radadin asarorin da suka yi.
Har zuwa shekaran jiya da maraice, wakilinmu ya yi iya ka yinsa don jin ta bakin hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Bauchi wato SEMA domin jin ta bakinsu kan shirye-shiryen gwamnati na samar da tallafi wa jama’a, inda hukumar ta shaida cewar har zuwa lokacin da muke hada wannan rahoton su basu kai ga kammala bincikensu ba, kamar yadda babban sakataren hukumar SEMA ya shaida mana.
Ita dai wannan Guguwar ta ranar Asabar 16/6/2018 ta yi mummunar barna, kamar yadda muka bayar da rahoto, idan aka kasa jihar Bauchi uku, biyu daga cikin ukun nan Guguwar ta barnata su.

Advertisement

labarai