Amai Da Gudawa Ya Kashe Sama Da Mutum 20 A Kebbi

Rahotanni daga jihar Kebbi na cewa, sama da mutum 20 suka rasa rayukansu sakamakon cutar amai da gudawa da ta barke a Kauyukan : Tungar Buzu, Korama,  Samanaji da Keri a garin Shanga, a karamar hukumar Birnin Kebbi, sai kuma Fakai a karamar hukumar  Koko/Besse.
A ranar litinin da ta gabata Maryam Umar ‘yar shekaru 14 ta mutu a sanadiyyar cutar amai da gudawa a kauyen Tungar Buzu, a kauyen Kardi kuwa an tabbatar da mutuwar mutum uku.
Mazauna kauyukan suna cikin fargaba saboda yadda cutar take saurin yaduwa a tsakanin kauyukan, ita Maryam Umar ta zo ziyarar sallah ne a kauyen Tungar Buzu inda ta kamu da cutar.
Exit mobile version