Jamil Gulma">

Ambaliya: Mun Dauki Matakan Raba Kayan Tallafi A Bagudo – Kaura Danhakimi

Karamar hukumar mulki ta Bagudo da ke jihar Kebbi ta ce ta dauki kwararan matakai wajen rabon kayan tallafi ga wadanda iftila’in ambaliya ya shafa a karamar hukumar.

Shugaban Karamar hukumar mulki ta Bagudo Honarabul Muhammadu Kaura Danhakimi ne ya bayyana haka a jiya Talata da ya ke zantawa da wakilinmu a garin Bagudo.

Kaura Danhakimi ya ce ya zama wajibi wajen mu da mu dauki kwakwkwarar mataki wajen rabon kayan tallafi ga wadanda iftila’in ya shafa saboda mu ne muka fi kowa samun matsalar ambaliya don mu ne matattar duk ruwanda ya zo sannan kuma mune mu ke da sarkawa da ke tu’ammalli da sana’ar kamun kifi wadanda ke zaune danganen kokuna kuma alhamdu lillahi saboda kwamitin da muka hada ya kumshi sarakuna,  malaman addini, jami’an tsaro, yansiyasa da kuma kungiyoyin sakai saboda haka muka sami nasara.

Advertisements

Wannan kwamitin a karkashin jagorancin Magajin Zagga Alhaji Mainasara Zagga, Sarkin Yamman Illo Alhaji Muhammadu Salah Illo, Sarkin Kudun Illo Alhaji Muhammadu Illo da Kuma Magajin garin Illo Alhaji Ibrahim Magaji wadanda su ne suka fi kusantar mutanen da abin ya shafa.

Kaura Danhakimi ya yabawa Uwargidan shugaban kasa Aisha Buhari, gwamnatin jihar Kebbi bisa ga daukar matakin gaggawa don kawo dauki ga wadannan bayin Allah inda ya kuma tabbatarda cewa tun lokacinda taimakon ya shigo aka soma rabawa.

Wannan Kwamitin bai tsaya a nan ba yana kwana cikin shirin ko-ta-kwana na rabon duk abinda ya shigo hannu a shirye suke da su baro gidajensu don isar da kayan ga wadanda ya kamata.

Ya kira ga wadannan sarkawan da kuma wadanda ke zaune danganen koguna da su canza mazauni zuwa wajen da ba za a samun barazanar irin wannan iftila’in ba su gina gidajensu na dindindin amma ba za hana su zama na wicingadi a wajen neman abincinsu na yau da kullum ba, da ya ke yanzu haka dai gwamnatin jihar Kebbi ta soma neman lalabo hanyar nema musu matsugunai na dindindin.

Daga karshe ya ce yanzu haka dai mutanen ba su cikin muguwar damuwa saboda ana ba su cikakkiyar kulawa tun kama daga abinci, kiwon lafiya, ruwan sha da  dai sauran kayan more rayuwa sannan kuma ana nema musu matsugunai na dindindin ba da dadewa ba.

 

Exit mobile version