Ambaliya Ta Barnata Gonaki 3,250 A Bade Da Ke Yobe – SEMA

Gonaki

Daga Muhammad Maitela

 

Shugaban hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Yobe (SEMA) Dr. Mohammed Goje ya bayyana cewa ambaliyar ruwan ta shafi sama da kananan hukumomi 10 a jihar Yobe. Ya ce duk da akwai bambanci a yanayin ambaliyar ruwan, amma daga ranar 5 zuwa 10 ga watan Oktoba ambaliyar ta fi tsanani a kananan hukumomin Bade da Jakusko a jihar.

Shugaban hukumar ya bayyana hakan a tattaunawar sa da wakilin mu a jihar Yobe, bayan ziyarar da tawagar hukumar ta kai tare da tantance kimar barnar da ambaliyar ruwan ta mamaye a yankunan kananan hukumomin Bade da Jakusko ranar Asabar.

Ya ce, “A karamar hukumar Bade ambaliyar ta shafi garuruwa 31, kuma a karamar hukumar Jakusko ta shafi garuruwa 52. Haka kuma ambaliyar ta mamaye gonakin jama’a baki daya, musamman inda abin ya yi muni shi ne a daidai lokacin da jama’a ke kokarin fara girbe amfanin gona. Kuma mu na kyautata zaton hakan ya zo ne ta dalilin tumbatsar kogin Hadeja, amma babu asarar rai.

“Bugu da kari, Bade kadai ambaliyar ta shafe gonakan shinkafa, lambu da hatsi na manoma 3250. Sannan kuma yanzu haka ma’aikatanmu su na kan aikin tattara bayanan adadin gonakan da wannan ambaliyar ta shafa a hukumar Jakusko,” in ji shi.

Dr. Goje ya kara da cewa Gwamnan jihar Yobe ya umurci hukumar kai kayan tallafin gaggawa ga al’ummar wadannan kananan hukumomin, na abinci da masarufi, wanda a matakin farko SEMA ta kai tirela shida (6) a karamar hukumar Bade, yayin da ake shirin aikewa da tallafin gaggawa zuwa karamar hukumar Jakusko, nan kusa. Ya ce, “Saboda la’akari da muka yi abincin rumbu ya kare kuma na gonar ambaliyar ta lalata.”

Mohammed Goje ya sanar da cewa, “baya ga wannan kuma, Gwamnan jihar Yobe, Hon. Mai Mala Buni ya hukumar SEMA ta tattara komatsanta ta koma karamar hukumar Bade da zama, daga ranar wannan Litinin mai zuwa har sai abinda hali yayi.”

A nashi bangare kuma, mukaddashin shugaban karamar hukumar Bade (DPM), Alhaji Adamu Dagona ya bayyana cewa, bayanan da suka tattara ya nuna sama da shekaru 60 ba a ga irin wannan ambaaliyar ruwa ba, wadda ta mamaye gidaje da gonakan noman damina da na kayan lambu da gonakan shinkafa, a wadannan garuruwan, tare da asarar dimbin dukiyar da Allah ne kadai ya san adadinta.

“Sannan kuma, bisa rahotanin da muka tattara a matsayin karamar hukuma, mun tura zuwa ga gwamnatin jihar Yobe da hukumar NEMA, hukumar NEDC, kuma nan take Gwamnan jihar Yobe, Hon. Mai Mala Buni ya umurci hukumar SEMA ta kawo wa jama’a tallafin gaggawa na kayan abinci da masarufi, wanda yanzu haka ana tattauna yadda za a raba kayan ga wadanda abin ya shafa.”

Alhaji Dagona ya yi kira ga jama’ar karamar hukumar Bade, cewa su guji yin gine-gine a kan hanyar ruwa, saboda don kaucewa matsalolin ambaliyar ruwan. Sannan ya ce, “kuma tun bayan yadda matsalar ta yi kamari muke kai gwauro-mari wajen kai daukin kayan aiki a yankuna daban-daban da kai ziyarar gani da ido tare da jajanta wa jama’a. Kuma muna kira ga jama’a a ci gaba da bamu bayanai a duk inda aka ga wata matsala.”

A hannu guda kuma, mukaddashin shugaban karamar hukumar Jakusko, Bakura Usman ya yaba da matakin daukin gaggawa da gwamnatin jihar Yobe ta dauka, na koken al’ummar su dangane matsalar ambaliyar ruwan, wadda ta shafi garuruwa sama da 50 a karamar hukumar, ya ce wannan abin a yaba ne.

“Gwamna Mai Mala Buni ya turo kwamishinan ma’aikatar kula da ayyukan jinkai da ibtila’i na jihar Yobe hadi da shugaban hukumar SEMA kuma mun zagaya wasu garuruwan da za a iya shiga kamar irin su Amshi, Dachia, Kazir da sauran su, kuma sun ga yadda ambaliyar ta mamaye gidaje da amfanin gonakan jama’a wanda kuma sun tattara bayanan garuruwan da matsalar ta shafa kuma suna ci gaba da aikin.”

Ya kara da cewa, ambaliyar ruwan ta jawo asarar dimbin dukiyar da ba za ta misaltu ba, ya ce sanin kowa ne karamar hukumar Jakusko ta kunshi manyan manoman da suka shahara a kowane fanni inda zaka samu mutum sama da 100 suna aiki a gonar manomi daya, kuma ambaliyar ta mamaye dukan abinda suka shuka a gonakan.

“Bisa ga hakan, mu na mika godiyar al’ummar karamar hukumar Jakusko bisa matakan gaggawar da Gwamna Mai Mala Buni ya dauka dangane da lamarin, wanda tun kafin abin ya kai ga haka, mun mika rahoto ga gwamnatin jihar Yobe kuma ta tallafa da kayan aiki don tunkarar matsalar, amma kuma abin ya fi karfin mu.” In ji shi.

Ya ce gwamnatin jihar Yobe ta bayyana daukar matakin tallafa wa wadanda ambaliyar ta shafa wajen rage girman asarar da suka tabka.

 

Exit mobile version