Connect with us

LABARAI

Ambaliya Ta Kashe Mutum 10 A Anambra

Published

on

Ambaliyar ruwa da ta shafi wasu sassa na Jihar Anambra, ta ci ran wata yarinya ‘yar shekara 9 mai suna, Benedict Uzo da ke garin Amiyi, ta karamar hukumar Ogbaru, ta Jihar.

Shugaban karamar hukumar ta Ogbaru, Mista Arinze Awogu, ya shaida wa manema labarai a ranar Laraba cewa, yarinyar ta nutse ne a cikin ruwan a kokarin ta na debo ruwa da bokiti.

Ya ce, ita ma yayar ta Benedict, mai shekaru 11, kiris da ta rasa ranta a kokarin da ta yi na ceto kanwar na ta, sai da makwabta suka yi kokarin ceto ta.

“Matsalar ta ambaliyar ruwan a karamar hukumar ta Ogbaru, a Jihar ta Anambra, tana ta ci gaba da fantsama, inda ya kai karamar hukumar ta Ogbaru ta rasa rayukan mutane biyu tun fakon farawan ambaliyan ruwan.

“Wacce lamarin ya rutsa da ita na baya-bayan nan ita ce, wata yarinya ‘yar shekara tara mai suna, Uzo Benedict Onyebuchukwu, wacce take aji na 3 a makarantar, ‘Light International School, da ke, Okoti.

“Mahaifin yarinyar mai suna, Izuchukwu Uzo, ya shaida mani cewa, ruwan ne ya yi awon gaba da diyar na shi a lokacin da ta yi kokarin diban ruwan a cikin bokiti.”

Shugaban karamar hukumar ya bukaci mutanan yankunan da ambaliyar ruwan ta shafa da su kaurace zuwa wasu amintattun wuraren ko kuma sansanonin ‘yan gudun hijirar da aka tanada masu.

“Wannan lokaci ne na bakin ciki a gare mu, muna kuma tabbatar wa da iyalan da lamarin ya shafa goyon bayanmu a wannan lokacin na tsanani a gare su, na yi alkawarin sanar da Gwamnan Jihar mu, Mai Girma, Gwamna Willie Obiano, kan wannan rashin da aka yi.

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: