Shanu da yawa sun kasance makale a saman rufin wani gidaje sakamakon ambaliyar ruwa a kasar Koriya ta Kudu, a inda ma’aikatan ceto suka yi ta fuskantar matsaloli wajen ceton dabbobi saboda irin girma da kuma yawansu.
Ambaliyar ruwan ya bar Shanun ne a saman rufin a karshen makon nan a Gurye, wani garin manoma a kudu maso kudancin kasar, kuma ya yi ta gudu zuwa rufin gidaje da dama da wasu gine-gine.
Lokacin da ambaliyar ta ja baya, dabbobin sun sami kansu cikin mawuyacin yanayi kuma da dan danshi, suna ta kuka ga shi babu hanyar sauka daga saman rufin.
Hotuna sun nuna kamar tara daga cikinsu suna tsaye a saman rufi kwano daya, sun yi laushi sosai. “Shanun suna ta iyo yayin da ruwan ya tashi da su har zuwa haurawa saman rufin, a inda suka yi tsaye can har bayan tsayawar ambaliyar,”in shi wani mazaunin garin.
Koriya ta Kudu ta yi ambaliyar ruwa makonni da suka gabata, wanda suka haddasa ambaliyar ruwa, inda aka samu mutuwar mutane sama da 31 tun farkon watan.