Connect with us

MANYAN LABARAI

Ambaliyar Ruwa Ta Ci Rayuka Tara da Gidaje 200 A Gwambe

Published

on

Akalla mutum tara ne suka rasa rayukansu, sannan gidaje 200 suka rushe, da gonakin noma masu yawa, sakamakon ambaliyar da ta afku tsakanin watannin Mayu zuwa Agusta na wannan shekarar a jihar Gwambe.

Hukumar bada agajin gaggawa ta kasa ta fitar da sanarwar da ke nuna mutum hudu daga cikin  tara da suka rasa ransu, ambaliyar ta rutsa da su ne a watan Mayu a cikin garin Gwambe sakamakon ruwan sama mai karfi da aka dinga yi.

Gidaje akalla 200, da gonakin noma masu yawa duk ambaliyar ta share su, musamman a kauyukan Nyuwar, Jesu Cham, Balanga da Komta Ayaba duk a cikin karamar hukumar Biliri ta jihar Gwambe.

A kauyen Cham kuwa na karamar hukumar Balanga an samu asarar rayukan mutum biyar a cikin watan Agustan da ya gabata, saboda ruwan sama da aka dinga yi kamar da bakin kwarya a watan.

Hukumar bada agajin gaggawa ta kasa ta ce, ta taimakawa wadanda abun ya shafa da kayan abinci, da sauran abubuwan more rayuwa da suka dace da wadanda suka shiga wannan halin an neman taimako.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: