Connect with us

LABARAI

Ambaliyar Ruwa Ta Ci Rayukan Mutane 14 A Neja, In Ji SEMA

Published

on

Akalla mutane goma sha hudu ne suka mutu a sakamakon ibtila’in Ambaliyar ruwa a jihar Neja.
Daraktan rage radadi na hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa reshen jihar Neja SEMA, Alhaji Garba Salisu shine ya shaida hakan a hirarsa da kamfanin dillacin labarai ta Nijeriya a garin Minna jiya Asabar, inda ya ce, mutune goma sha hudun sun mutu ne a sakamakon ambaliyar ruwa a sassa daban-daban na jihar.
Ya kara da cewa; hukumarsu ta aiwatar da aiyukan agaji ga akalla al’ummomi 200 da lamarin ya shafa domin ceto su daga musifar.
Ya kara da cewa jami’ansu na masu aikin ceto za su ke taimaka wa a dukkanin lokacin bukatar hakan.
Salisu ya roki mazauna jihar da suke kokarin baiwa kwalbati-kwalbati sarari domin ruwa yake samun yanayin wucewa ba tare da ya yi barna wa jama’a, yana mai bukatar jama’a da su daina zubar da shawara a cikin magudanan ruwa domin rigakafin ambaliyar ruwa a fadin jihar.
Daga bisani ya bukaci al’ummomin da suke rayuwa a kusa da wuraren da ruwa ke kwaranya da su sauya muhallai domin kauce wa barnar amaliyar ruwa a tsakanin al’umma.
“Manyan ababen da muke jin tsoronsu su ne, mafi yawan lokuta ana samun ruwan sama da karfi a cikin dare a lokacin da jama’a ke kwance suna barci, a duk lokacin da ruwan sama ya zo ya tarar da magudanar ruwa an cikasu da shara zai nema a kansa hanya ne, daga wannan wurin kuma barna zai je ya yi, don haka dole ne muke tsaftace muhallanmu domin kariyan kai,” Inji shi
Ya shawarci jama’a da su daure su kaurace wa dukkanin wuraren da ka iya jefa su cikin Ambaliya hadi da tabbatar da tsaftar muhallai a kowani lokaci.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: