Connect with us

MANYAN LABARAI

Ambaliyar Ruwa Ta Ci Rayukan Mutum Tara A Jihar Kano

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta tabbatar da mutuwar tara da wasu biyar da suka samu raunuka a ambaliyar ruwa da ta shafi  wasu kananan hukumomi tara da ke jihar.

Babban Sakataren hukumar agajin gaggawa na jihar ya tabbatar da cewa ambaliyar ta shafi akalla mutum 4475 a fadin kananan hukumomi tara da abun ya shafa, mutum biyar sun rasa ransu a Rimin Gado, mutum uku a Gabasawa, sai mutum daya a garin Getso da ke karamar hukumar Gwarzo.

‘Mutum tara Kenan suka yi asarar rayukansu, a yayin da wasu mutum biyar kuma suka samu raunuka, zuwa yanzu an tabbatar da abun ya shafi mutum 4,475, duk da har yanzu ba a gama tamntance wadanda abun ya shafa ba, ana kan tattaro bayanai daga karin kananan hukumomi biyar.’ Inji Sakataren

Ya kara da cewa, ambaliyar ta bi ta kananan hukumomi 14 ne, amma zuwa yanzu bayanan kananan hukumomi tara muka iya hadawa, sauran kananan hukumomi biyar din ma muna sa ran kammalawa cikin lokaci, muna hada rahotanni ne don mu mika su gwamnatin jiha don daukar matakin da ya dace.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: