Connect with us

MANYAN LABARAI

Ambaliyar Ruwa Ta Hallaka Mutum Goma A Jihar Anambara

Published

on

Ambaliyar ruwan da ta afku a jihar Anambara ta yi sanadiyyar mutuwar wata yarinya ‘yar shekaru tara, mai suna Uzo Benedict a kauyen Amiyi dake karamar hukumar Ogbaru a yau Laraba 26 ga watan Satumba 2018.

Al’amarin ya faru ne a yayin da yarinyar ta je dibar ruwa tare da yayarta ‘yar shekaru 11 da haihuwa, yayar ta yi kokarin ceto ran kanwarta, amma haka ya jawo ta kusan yin asarar rayuwarta ita ma, cikin taimakon Allah makwota suka ceto ta.

A cikin kwanakin nan ambaliyar ruwan ta kara Kamari, a inda wasu mutum biyu suka rasa ransu a jiya, a yau kuma Uzo ta rasa ranta, wannan ya kawo adadin wadanda suka rasa ransu ya kai mutum 10.

hukumomi suna ta kokarin ankarar da mutane da yankin da ambaliyar ta fi shafa da su yi kokari barin wajen na dan wani lokaci, saboda a rage asarar rayuka da dukiya da ambaliyar take haifarwa.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: