Connect with us

MANYAN LABARAI

Ambaliyar Ruwa Ta Kashe Mutum Shida A Katsina

Published

on

…Ta Raba Mutum 1,000 Da Muhallinsu

A yammacin shekanjiya ne Alhamis wani irin ruwa da iska wanda al’umma suka ce an manta rabon da a ga irinsa ya yi mummunar barna a cikin garin Katsina a wasu unguwannin guda bakwai.

Mamakon ruwa dai ya yi sanadiyar kashe mutum shida a wurare daban-daban sannan ya raba fiye da mutum dubu da muhallinsu wanda yanzu haka suna cikin wani irin halin na ni ‘ya su.

Wasu daga cikin unguwannin da manema labarai suka kewaya domin ganin irin barna da ruwa da iskar suka yi sun tarar da jama’a na ta alhinin wannan iftila’i da ya fada masu, a yayin da aka kai wasu asibitoci wasu kuma wajen masu dorin gargajiya domin neman lafiya.

Wannan mummunar iska ta fi yin barna a unguwar Kukar gesa da Shinkafi da Modoji da Gidan kwakwa da Malali da Rafin dadi da Sabon titin kwado da sauran unguwanni inda bayan lalala dukiyoyi ta hada har da kashe jama’a.

Wasu da wannan iftila’in ya afkawa sun bayyana irin yadda suka ji da wannan jarabawa da suka ce tunda suke ba su taba ganin iska da ruwa irin wannan da aka yi shekaranjiya Alhamis ba.

Dakta Muhammad Na’im wanda ya ce sun ta shi da wannan al’amari  da ya ce jama’a da dama sun rasa muhallisu sakamakon wannan barna da ruwa mai iska ya yi unguwar Sabuwar Malali inda a nan yake shugaban kungiyar ci gaban wannan unguwa.

Ya kuma kara da cewa, bango ya fadawa mutane da dama inda suka yi aikin ceto suka fito da wasu mutane,ya ce kasancewarsa ma’aikacin jinya ya taimaka matuka gaya wajen ceto rayukan wasu inda nan take aka ba su taimakon gaggawa kafin daga baya akai wasu asibiti.

Dakta Muhammad Na’im ya ci gaba da cewa wasu mutanen a gidansa suka kwana, daga nan sai ya yi kira ga gwamnati da ta dubi wadanda wannan bala’i ya fada wa da idonun rahama wajan ba su taimakon gaggawa.

Shi ma Mustapha Yusuf yana daya daga cikin wadanda gidansa ya rushe dukka kuma yana zaune ne a unguwar Sabuwar Malali ga abin da yake cewa, ‘’Shekaranjiya da yamma muna zaune sai kawai muka ji iska wanda ba mu taba ganin irinta ba tunda muke, mun ga gidajan da suka fadi a wannan unguwa Kaiwa sun kai dari uku.’’ In ji shi

Haka shi ma wani dan kasuwa da yake sayar da kayan miya a kasuwar ‘yan gwari da ke Katsina, mai suna Salisu Alkasim ya bayyana cewa runfarsa ta kasuwa ta rushe kuma ya ji labarin abin da ke faruwa sai dai lokacin da ya isa gida ya tarar gidansa ya fadi jama’a kowa ya yi ta kansa.

Sai dai ya ce wannan al’amari daga Allah yake saboda haka ya maida komai gare shi kuma yana kira ga gwamnatin jihar Katsina da ta taimakamasu a kan wannan iftila’I daya afka musu.

Ita kuwa Malama Farida ta ce wannan abu da ya zo musu daga Allah ne dakuna biyu da suke gidanta sun rushe duka daman dayan ya rushe tun tuni, yanzu kuma dayan ya karasa yanzu dai ba su da matsugunni na zama kuma yanzu maganar da ake yi mai gidanta ba ya garin ya tafi jihar Neja neman kudi.

Ya zuwa yanzu jama’a da dama suna ta yi kaura domin kusantar ‘yan uwansu domin samun matsugunni a yayin da suka rasa na su muhallin wanda yanzu a nata bangaran gwamnati ta ce ta fara aikin tantance wadanda wannan bala’I ya fadawa domin ba su tallafin gaggawa.

Shugaban hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Katsina Dakta Aminu Garba Waziri ya tabbatar da rasuwar mutum shida sannan ya kara da cewa jama’a da dama sun rasa muhallinsu a unguwanni da dama da wannan ambaliyra ruwa ta shafa a garin na Katsina.

Ya kara da cewa unguwar Kukar gesa mutum hudu suka mutu, wasu da dama suka jikkata sai kuma unguwar Modoji nutum biyusuka rasu nan ma wasu suka jikkata wanda yanzu haka suna asibiti domin karbar magani.

Dakta Aminu Waziri ya ce gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari ya ba su umarni su yi kididdiga ga jama’ar da wannan iftila’I ya fadawa domin sanin hakikanin abin da ya faru tare da bada tallafi a gare su, hatta abin da hukumar take bukata gwamnati ta shirya tsaf domin taimakawa.

A cewarsa bisa ga rahotannin da suka samu fiye da mutane hamsin sun rasa muhallinsu inda suke tunanin  za su sama ma su wani matsuguni na daban, sai dai ya ce yanzu haka suna zaune a wata islamiyya a cikin unguwar Kukar gesa.

Haka zalika ya ce sauran unguwannin da wannan iftila’I ya fadawa tuni aka tura jama’ar hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Katsina domin yin kididdiga domin tantace irin yawan asarar da aka tafka sakamakon wannan ruwa mai iska da rwan sama mai tsananin karfin gaske.

 
Advertisement

labarai