Daga Zubairu M.T Lawal, Lafia
Ranar Alhamis din da tagabata ne ambaliyar ruwan ta yi sanadiyya mutuwar wani yaro dan shekarar shida a Unguwar Nungu cikin garin Lafiya. Ambaliyan ta biyo bayan ruwan sama da aka tafka kamar da bakin-kwara da daddare.
Wakilinmu da ya ziyarci gurin da abin ya faru, ya zanta da iyayen yaron da kuma sauran al’ummar Unguwan kamar haka; Sunana Muhammad Ibrahim ni ne mahaifin wannan yaron mai suna Shatima Muhammad.
kuma wannan yaron ba shi ne na farko da ruwan sama ya yi sanadiyyar mutuwarsa ba, a nan Unguwar. Saboda duk lokacin da muka ga hadari hankalinmu kan tashi. saboda yadda ruwan yake zuwa a layinmu kuma ga wannan wawakeken rami da yake kara rusa gidajen jama’a.
Ita ma da take zanta wa da wakilinmu, mahaifiyar marigayi Shatima, mai suna A’ishatu Muhammad ta ce, ranar Alhamis muna kwance cikin dare ana ruwa duk hankalinmu ya tashi. Sai muka ji rushewar katangar gidanmu mun fita jama’a kowa nayin ta kansa da yaransa.
Lokacin da na fito sai na tarar kowa ya gudu na dauko yarona muna fita sai na yi karo da wani abu amma sai na wuce ruwa ya yi yawa ga duhu kafin na kai bakin kofar gidan na bude sai nafadi, a cikin gidan sai ruwa ya kama tafiya da ni shi kuma yana goye a bayana.
Ruwa na tafiya da mu ya shige da mu cikin wannan katon ramin yana ta tafiya da mu har cikin wani kurmi, gurin da babu wanda zai iya zuwa wajen cikin daren nan. Haka ruwan ya yi ta tafiya da mu yana ta wuntsulamu babu yadda zan yi na rungume yaron sosai ruwan na tafiya da mu. Cikin haka, sai yaron ya kubce a hannuna, ruwa ya rika tafiya da shi, ta ce tana kallo ruwa yana tafiya da yaronta babu yadda ta iya.
Ita ma Allah ne ya sa kwananta na gaba sai ta yi karo da wata bishiya da ruwan ya kayar ba, nan ne ta tsaya babu komai a jikinta sai karamar riga. Tana ta adu’a idan ta ga hasken kamar na tochila sai ta kwalla ta yi ihu saboda ko jama’a za su ji ta, amma babu wanda ya ji ta.
Daga nan sai ta ji muryar wasu mutane sai ta yi ihu sai suka zo suka ce waye a nan ? na ce ni ce, ruwa ne ya tafi da ni ku taimake ni. Ta ce, da kyar suka iya fito da ni daga wannan gurin.
Amma yaron tun da na ga yadda naga ruwa yake tafiya da shi, na sallama na san ya mutu saboda yadda ruwan yake yi da mu a cikin kurmin ramin nan Allah ne ya sa kwanana na gaba. An tsinci gawar yaron a Wambi da ke Unguwar Poly washe gari.