Ambaliyar Ruwa Ta Mamaye Makabarta A Gashuwa

Daga Muhammad Maitela,

Sakamakon ruwan sama mai karfi da aka yi kamar da bakin kwarya da safiyar ranar Litinin, ambaliyar ruwa ta mamaye wani bangaren babbar makabartar garin Gashuwa, shalkwatar karamar hukumar Bade a jihar Yobe.

Ruwan ya mamaye kimanin kaburbura 650 da ke cikin tsohuwar makabartar, wanda hakan ya jawo rushewar wasu da dama daga cikin wannan adadin, tare da faduwar bangaren katangar da ta zagaye wurin, wadda wajen yashi ne.

A zantawar sa da wakilinmu a jihar Yobe, shugaban karamar hukumar Bade, Alhaji Sanda Kara-Bade ya tabbatar da faruwar al’amarin tare da bayyana daukar matakan gaggawa wajen aiki da yan sa kai daga kungiyoyin agaji da sauran al’ummar gari don bayar da taimako don takaita barnar ruwan a makabartar.

“Haka kuma mun shaida wa gwamnatin jihar Yobe halin da ake ciki, wanda nan take ta dauki matakin gaggawa wajen tura kwararru domin daukar matakan kawo karshen malalar ruwa a makabartar.” in ji shugaban karamar hukumar Bade.

Dangane da halin da ake ciki, Gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe ya bai wa hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Yobe (SEMA) umurnin sake gina makabartar.

Shugaban hukumar (Edecutibe Secretary), Dr Mohammed Goje, shi ne ya bayyana haka ga manema labarai a Damaturu tare da sanar da cewa sun fara shirye-shirye, tattara kayan aiki da kwararru don fara aikin sake gina makabartar kamar yadda Gwamnan ya bayar da umurni.

“Mun fara shirye-shiryen aikewa da bulo da siminti tare da sauran kayan aiki don gyara makabartar cikin hanzari.”

A batu na daban kuma, wannan ba shi ne karon farko ba wanda ruwa ke mamaye makabartar tare da rusa makwantan, wanda hakan bai rasa nasaba da karancin magudanun ruwa a garin na Gashuwa, musamman wasu hanyoyin da aka gina ba tare da magudanun ruwa ba, kana da yadda jama’a ke ci gaba da gine- gine ba bisa ka’ida ba.

Exit mobile version