Abubakar Abba" />

AMCON Ta Karbo Naira Tiriliyan 1 Daga Masu Bashi A Cikin Shekara 8 –Gwamnatin Tarayya

Minstar kudi uwargida Zainab Ahmed ta sanar da cewar, tun kokacin da AMCON ta fara gudanar da ayyukanta a shekarar 2010 ta samu nasarar karvo kimanin naira tiriliyan daya daga gun wadanda sukaci bashin bankuna. Uwargida  Zainab Ahmed ta sanar da hakan me a garin  Abuja kokacin da take kaddamar da kwamitin amintattu na AMCON a karkashin shugabancin Mista Muiz Banire (SAN).  Gwamnatin Tarayya ce ta kafa AMCON ta hangar Babban Bankin Nijeriya CBN doon kuvutar da bankunan dake kasar nan ta hanyar sayen basussuka   da basa yin wani katavus da kuma karvo basussukan data gun wadanda suka karva. Acewar Zainab  Ahmed, daga cikin basussukan da AMCON ta karvo na gudarin kudi sun kai kashi 60 bisa dari, inda kuma kadarori sun kai kashi 40 bisa dari. uwargida  Zainab Ahmed ta ci gaba da cewa, duke a lokacin, AMCON ta biya dukkan basussukan ga Babban Bankin Nijeriya CBN na sama da naira tiriliyan daya ,inda kuma jimlar bashin a yanzu ya kai naira tiriliyan biyar. Minista Zainab Ahmed ta kara da cewa, idan akayi la’akari da yanayin tattalin arzikin kasar nan, Gwamnatin Tarayya bazata iya yafe bashin ba na gajeren zango. Ministar ta shawarci  sabon kwamitin amintattun na su fito da tsare-tsare da zasu taimaka wajen karvo dauwkacin basussukan da kuma kadarorin, ganin cewar Gwamnatin Tararray ta Cora masu nauyin yin hakan. Acewar uwargida  Zainab Ahmed, run likacin da aka kafa AMCON ta samo samada basussukkn da suka NASA yin katabus had guda 12,000 da kudin su ya kai naira tiriliyan 3.7 daga bankuna guda  22 tare da zuba naira tiriliyan 22 a bankuna goma. Ta ce, hakan ya yi alfanu India za’a iya ganin yadda aka bayar da kariya kimanin ta naira  tiriliyan 3.66 ga masu ajiyar kudi son kirkiro da ayyukanta guda 14,000. Ministar ta yi nuni da cewar, abun a zahiri take Gwamnatin Tarayya bazata iya yafe basussukan ba a cikin gajeren zango kuma AMCON ba za ta gajiya ba wajen ganin ta karbo daukaci bashin. Ta bayyara cewar, Gwamnatin Tarayyar zata yi dukkan mai yuwa wajen ganin ta karvo daukacin bashin.

Exit mobile version