Amfani Da Harshen Gado: Kowa Ya Bar Gida, Gida Ya Bar Shi (I)

Domin kiyaye asali da a ka gada iyaye da kakanni, Majalisar Dinkin Duniya ta kebe kowace ranar 21 ga Fabarairun kowace shekara ta zama ranar bikin harshen gado ko a ce harshen asali ko a ce harshen uwa (dai-dai gwargwadon fahimtar mutum). An kebe ranar ce domin ta saje da 21 ga Fabarairun 1952 wacce a cikinta babban abin bakin cikin nan ya faru na kashe yara kanana hudu a Dhaka, Babban Birnin Bangaladash, saboda rikicin harsunan Bengali da Urdu. Tun daga shekarar 2000 da a ka fara bikin ranar, duk shekara sai an yi a duk fadin duniya. Babban makasudin bikin ranar dai shi ne a yi rigakafin bacewar harshen gado daga doron kasa kamar yadda abin ya shafi wasu yaruka kuma yake cigaba da shafar wasu a duniya; ciki har da mu a nan Nijeriya.

Wani bincike da Kungiyar Masana Harshe ta Amuraka ta gudanar a shekarar 1996, ya bayyana cewa akwai yaruka da ake magana da su a duniya guda dubu shida da dari bakwai da uku (6,703). Daga cikin wannan adadin, ana magana da guda dubu biyu da goma sha daya (2,011) a Afirka, guda dubu biyu da dari da sittin da biyar (2,165) a yankin Asiya, sai dubu daya (1000) a Amurka, da dubu daya da dari uku da ashirin a yankin Fasifik da Astareliya (1320), kana yankin Turai yana da yare guda dari biyu da ashirin da biyar (225) da ake magana da su. Wasu masana harshe sun yi amannar cewa adadin yawan yarukan zai ragu da kusan rabi ko kuma su tashi daga dubunnai zuwa daruruwa, sakamakon karancin masu magana da yarukan, inda hakan ke kara bude kofar mamayar manyan yarukan duniya irin su Larabci, Turanci, Sifaniyanci, Mandarin (Sinanci), Indiyanci, Swahili da sauransu. Masana harshen ba su tsaya nan ba, har ila yau sun yi kashedin cewa nan da karni guda mai zuwa, kusan kashi 80 a cikin dari na yawan yarukan duniya za su bace.

Yarukan da suka fi fuskantar barazanar bacewa bat a doron kasa su ne na al’ummomin da ba su da mutane da yawa, kuma a cikinsu ne dama aka fi samun yawan yarukan duniya. Wadannan yarukan sun hada da na Kabilun Fafuwa da ke Sabuwar Guinea wadda a cikinsu kawai akwai yaruka daban-daban sama da dari tara (900), sai Kabilun Aborijinal na Astareliya wadanda aka yi hasashen kashi 80 a cikin dari na yarukansu za su bace ba da jimawa ba saboda sauyin zamanin da ya danne su suka kasa motsi. Wakazalika, barazanar bacewar harshen ta kuma dumfari mutanen da suka kasance asalin Amurkawa da suka rike asalinsuna na yare da al’adu da kashi 90 a cikin dari, sai kuma wasu kananan yaruka a Afirka, da Asiya, da kuma wadanda masu rinjaye suka danne su a yankin Turai irin su Kabilun Irishawa (Irish), Firisiyawa (Frisians), Furobinkalawa (Provencal) da kuma Kabilar Baskiwo (Basques).

A shekarar 2012, Hukumar Kula da Ilimi da Al’adu ta Majalisar Dinkin Duniya (UNESCO) ta yi gargadin cewa akwai yarukan Nijeriya da yawa da za su iya bacewa a doron kasa nan da shekara hamsin masu zuwa. Saboda ‘yan asalin wadannan harsunan ba su amfani da harshensu nagado, sun gwammace su rika magana da harsunan kasashen waje.

Babban abu na farko da yake salwantar da harshen gado a doron kasa ya zama babu kamar ba a taba yinsa ba shi ne rashin koyar da yara manyan gobe harshen, ko kuma za a koyar din amma ga yara ‘yan kalilan, da rashin amfani da harshe wurin mu’amalar rayuwa a tsakanin manyan da suke magana da harshen da kuma yin biris da lalubo hikimomin da za a yi amfani da su wurin raya harshen. Sakamakon haka sai a wayi gari an yi jana’izar harshe bakidaya daga doron kasa.

Idan al’umma ta yi sake yarenta ya bace, to ta tafka asarar babban abin da za ta kafa shaidar gado da shi da nuna asalinta.

Kasancewar mu a nan Nijeriya, an karfafa yin amfani da manyan yarukan kasa guda uku, Hausa, Yarbanci da Ibo. Mukalata za ta fi karkata ga abin da ya shafi amfani da Hausa a matsayin harshen asali, saboda rubutun ma da Hausa nake yi, sannan wadanda ake yi dominsu (masu karatu) masu jin Hausa ne.

Kowa ya san hanyar neman ilimi ita ce babba wurin rayar da harshe, domin duk abin da mutum zai yi a rayuwa, zai yi amfani ne da ilimin da ya sani. An dauki matakin raya harshen Hausa a matakin ajin farko na makarantar firamare wadda ita ce ta farko bisa tsarin jadawalin makarantu na gwamnati a Nijeriya a yankin Arewa, kamar yadda aka yi wa Yarbanci a yankin Kudu-maso-yamma da kuma harshen Ibo a yankin Kudu-maso-gabas.

A sakamakon binciken da ya gabatar dangane da amfani da harshen Hausa a makarantun firamare na Jihar Kaduna a watan Disambar 2013, wani Malamin Hausa da ke koyarwa a Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Kaduna, Malam Is’haq Idris Guibi, ya bayyana cewa, “Tsarin ilimi na Nijeriya na shekarar 2004 wato (National Policy on Education), ya ce za a tabbatar da kowanne yaro da aka sa shi a makarantar Firamare, an koyar da shi da harshensa na gida a shekaru uku na farkon koyar da shi. Da ke nufin idan an sa yaro a Firamare ana bukatar a koya masa dukkan darussa da Hausa. Shin haka ake yi kuwa ko kuwa ba a yi? Na sha jin iyayen yara suna korafin za su cire ‘ya’yansu daga wata makaranta zuwa wata, wai sun ji ana koyar da ‘ya’yansu da Hausa, su kuma wai ba sun kai ‘ya’yansu a koya musu Hausa ba ne. Turanci zalla suke so domin a wajensu shi ne karatu”.

Yana da matukar ban-takaici a ce iyaye da kansu suke aikata hakan, daga bangaren mahukuntan makaranta kuma idan dalibi ya yi magana da harshensa na gado a makaranta za a hukunta shi. Sannan yawancin ‘yan asalin yaren da suke tutiyar sun yi karatun boko mai zurfi da ya kamata su zamo a kan gaba wajen kare harsunansu na asali, abin bakin ciki su suka fi kyamar amfani da harshen.

Ina da yakinin masu irin wannan tunanin sun gaza wajen fahimtar cewa kasashen da suke samun cigaba a duniya, suna amfani ne da harsunansu na gado. Malam Gubi bai wahalar da mai karatu ba, ya kawo jerin wadannan kasashen a cikin binciken nasa.

“Tsarin ilimi na kasa, wata tsararriyar hanya ce da kasa kan shirya domin cimma manufofin cigabanta. Saboda duk gwamnatin da ta san me take yi, ta san Harshe muhimmin abu ne na kyautata huldar zamantakewa, da hadin kan kasa da kare al’adu da dabi’un jama’arta. Tun shekarar 1977 gwamnatin Nijeriya ta yi wannan tsari cewa za a tabbatar da an koyar da yaro da harshensa na gida a shekaru uku na farko. Wasu suna da tunanin harshen Ingilishi ai shi ne harshen ilimi, harshen wayewa, idan ba ka iya shi ba, tamkar kai bi-can ne.

“Masu irin wannan tunani suna ganin harshen Ingilishi shi ya fi fice bangaren cigaban zamantakewa, da tattalin arziki, da kimiyya, da fasaha, da al’adu, da dabi’u. Sun ce wai a duk duniya masu magana da harshen Ingilishi sun fi yawa. Su kansu manyan da suka zauna suka yi wannan tsari, da baki ce kawai, su ne kan gaba wajen sanya ‘ya’yansu a makarantu masu tsada da turawa ke koyarwa, inda za su tashi da dabi’un da suka saba wa addininsu da falsafar iyayensu.

“A kasar Tanzaniya, suna amfani da harshen Swahili wajen koyar da ‘ya’yansu karatun boko, kuma dole ba zabi, da ya yi matukar taimaka wa cigaban kasar. Haka nan kasashen da ake ganin su ne, suka fi duk wata kasa ta duniya cigaba, su Birtaniya, da Rasha, da Faransa, da Sin, da Jafan suna amfani ne da harsunansu wajen koyar da ‘ya’yansu a makarantunsu na Firamare, da Sakandare, da jami’o’insu. Idan ka tafi Rasha, ko Sin, ko Jafan domin karatun likita, ko injiniyanci, dole sai ka koyi harsunansu, domin da harsunan nasu ne za a koyar da kai.

“A Nijeriya kuwa, ana koyar da karatun likita, da na injiniyanci, da ilimin kere-Kere da na fasaha cikin bakon harshe na ‘yan mulkin mallaka. Wannan ya sa ga mu nan jiya I yau. Mun samu ‘yanci amma ta fannin harshe har yanzun muna nan a matsayin bayi. Muna tinkaho da alfahari da harshen da ba namu ba, alhali babu abinda harshen nasu ya fi Hausa da shi. Hausa tana daya daga cikin manyan harsuna uku da ke da karfi da ake da su a Afirka. Hausa da Swahili da Larabci. Kasashen da ke yankunan Swahili, da na Larabci duk suna karatun boko ne da Swahali ko Larabci, amma ba inda ake koyar da karatun boko da Hausa, ko ana yi, bai taka kara ya karya ba”.

Bayan haka, daga cikin matsalolin amfani da harshen Hausa da binciken Malamin ya gano a makarantun firamare na Jihar Kaduna akwai: Yawancin makarantun firamare da ke jihar ba sa aiki da wannan tsari da ya ce a koyar da yara da harshensu na gida (Hausa), a shekarunsu uku na farko a firamare. Yawancin shugabannin makarantun firamare da ke jihar ta Kaduna suna sane da wannan tsari amma ba sa aiki da shi. Iyayen yara da su kansu yara, ba sa ba da hadin kai ga makarantu su ji dadin aiwatar da tsarin. Babu isassun malaman da za su iya koyarwa da Hausa a yawancin makarantun firamare da ke jihar Kaduna. Babu wadatattun kayan aikin koyar da darussan da Hausa a yawancin makarantun firamare da ke jihar. Babu isassun littattafai na koyar da darussan cikin harshen Hausa. Wadanda aka dora wa alhakin zagayawa domin tabbatar da ana aiki da tsarin ilimi ba sa aikinsu a jihar Kaduna. Ita kanta al’uma ta jahilci wannan tsari. Kasancewar akwai wasu kananan kabilu a jihar Kaduna, ya hana amfani da Hausa wajen koyar da darussan kamar yadda ya kamata.

Tabbas tun da akwai wadannan matsaloli jibge, illolin da suke haddasawa ba za su lissafu ba, matukar ba a dauki matakin da ya dace na rage su ba. Kadan daga cikin illolin da binciken Malam Guibi ya gano sun hada da: Ci gaba da raina harshen Hausa. Nuna ba a fadi da cikawa bangaren ilimin kasar nan musamman Gwamnati. Shafar cigaban adabin baka da na rubuce na Hausa. Cutar da yara ‘yan makaranta su rasa madafa saboda an rikita musu kwakwalwarsu da bakon harshe, da labarai da suka saba wa na muhallinsu da dabi’unsu. Ci gaba da dankwafar da malaman da suke koyar da Hausa. Ci gaba da hana wadanda ke da sha’awar karanta Hausa zuwa karanta Hausar. Ci gaba da zama kangin bauta wa wani harshe da ba naka ba. Bautar da kai kanka da tunaninka ya koma irin na Bature. Ya sanya yawancin yara suna ta faduwa jarabawar shiga sakandare saboda rashin iya Ingilishin da aka tilasta musu. Hana cigaban kimiyya da fasaha, da siyasa, da tattalin arziki da kere-kerenmu. Hana bunkasa harshenmu na Hausa. Ya sanya ma’aikatan rediyo, da talabijin, da jaridu har da Intanet suna kwaba Hausa yadda suka ga dama.

Idan har ana so a shawo kan wannan matsala, ba gwamnati kadai za a bar wa jan aikin gyara ba, duk wani dan asali yana da gudunmawar da zai bayar.

Da farko, a cikin dukkan yare, ya kamata iyaye su fara koyar da ‘ya’yansu harsunansu na asali tun daga lokacin da suka haife su. A karfafa gwiwar yaran su rika magana da harshensu na asali da nuna musu muhimmancin abin. A rika ba su labaru ko yi musu wake-wake da harsunansu na asali. Iyaye su karfafa kallon finafinan da suke kumshe da balaga da al’adu na harshen asali. A cusa wa yara son harshensu na asali tun suna kanana ba sai sun yi girma ba.

Ta bangaren amfani da harshen Hausa kuma, binciken Malam Guibi ya hutar da mu, kasancewar ya ba da mafita kamar haka: Gwamnati ta mike tsaye wajen tilasta aiki da tsarin koyar da yara karatun boko da harshen Hausa. Horas da malaman firamare iya koyar da darussa cikin harshen Hausa. Samar da littattafai na dukkan darussa da ake koyarwa a firamare cikin harshen Hausa. Samar da dukkan kayan aiki da ake bukata domin koyarwa da Hausa. Wayar da kan iyaye da duk sauran wadanda abin ya shafa, muhimmancin koyar da yara da harshensu na gida ta la’akari da kasashen da suka cigaba saboda amfani da harshensu. A mike tsaye wajen shirya tarurrukan bita da na kara wa juma ilimi akan muhimmancin koyar da karatun boko cikin Hausa. Farfesoshi na Hausa da sauran ‘yan boko da ke da kishin Hausa, su cire hassada da bakin ciki da mugunta da kananan maganganu, su yi tsayin daka wajen tabbatar da ana aiki da wannan tsari. A hana ladabtar da yara ko cin su tara idan sun yi magana da Hausa a makaranta. Ma’aikatar ilimi ta dage ta cije, da daure wandonta katakam domin sanya ido a kan makarantu don tilasta aiki da tsarin. Iyaye su daina cire ‘ya’yansu daga makaranta da sunan sun ji ana koyar da su da Hausa.

Za mu kwana nan, amma kafin diga aya, yana da matukar kyau al’umma ta san cewa kowa ya bar gida, gida ya bar shi. Ba zai yiwu a tambaye ka asalinka ka fada amma kuma nuna asalin naka ya gagare ka sannan mutane su dauke ka a matsayin sahihi mai tinkaho da asali ba. A kashi na biyu na wannan rubutu, za mu ji ta bakin wata Farfesar Harshe a Nijeriya game da tsara manufofi na amfani da harshen gado. Sannan mu dubi irin matsalolin da Malaman Hausa ke fuskanta a Sakandare.

Exit mobile version