Daga Muhammad Maitela, Maiduguri
Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, hadi da shugaban hukumar bayar da agajin gaggawa na kasa da kasa, Mista Mark Lowcock sun bayyana ci gaba da amfani da kungiyar Boko Haram ke yi na amfani da kananan yara wajen kai hare-haren kunar bakin-wake babban abin damuwa ne, saboda da yanzu haka sama da kananan yara 80 ne wannan ibtila’in ya rutsa da su ta hanyar dana masu bama-bamai, wanda yayi sanadiyar mutuwar sama da mutane 20,000 a yankin Arewa Maso-Gabas cikin shekaru takwas.
Mista Mark ya yi wannan furucin ne ga manema labarai, jim kadan da kammala wata tattaunawar sirri tsakaninsa da mataimakin gwamnan jihar Borno Alhaji Usman Mamman Durkwa.
Lowcock ya fayyace makasudin wannan ziyarar a cikin yankin hadi da gabar tafkin Chadi, domin auna girman bukatar da ake da ita ta bada tallafi ga al’ummar da wannan al’amari ya shafa kai tsaye. Kana da lalubo muhimman hanyoyi da za a bi kan lamarin, sannan da tantance tasirin ayyukan Majalisar Dinkin Duniya da takwarorinta a yankin tare da gano sauran wasu matsalolin da ake da su domin daukar matakin bai-daya wajen magance su.
Kamar yadda ya bayyana, Majalisar Dinkin Duniya hadi da takwarorinta masu bada agajin gaggawa, za su taimakin gwamnatin Nijeriya (da jihohi) wajen bada tallafi ga al’ummun da wannan ja’ifar ta shafa a ilahirin yankin da a matsugunan yan gudun hijira, gefe guda kuma da muhallanbda al’ummar sa dawo da zama.
Ya ce, “Na kawo wannan ziyarar ne domin jawo hankalin duniya da hadin gwiwa wajen kara azamar bada gudumawa ga yankunan da matsalar tsaron ta shafa, musamman mata da kananan yara, don ganin sun samu cikakkiyar kariya, ingantaccen abinci da dakile kamuwa da cutuka, misali don gujewa irin abinda ya faru a cikin yan kwanakin nan na cutar kwalara da ta abku a mafi yawan matsugan ‘yan gudun hijira.”
“Yanzu haka kimanin mutum miliyan 17 ne ke bukatar agaji a gabar tabkin Chadi, da suka hada da kimanin mutum miliyan 8.5 Arewa Maso Gabashin Nijeriya, alhalin kuma akwai kimanin mutane miliyan 5.2 da ke fuskantar barazanar karancin abinci a wadannan jihohi uku na Borno, Adamawa da Yobe, musamman idan aka hada da kimanin kananan yara 50,000 dake fama da karancin abinci mai gina jiki.” In ji shi.