Amfani Da Rashin Amfanin Kwalliyar Fuska Ta Amare

Kwalliya

Shafin Taskira na wannan makon ya yi duba ne game da irin kwalliyar fuskar da ake yi wa Amare wato ‘Makeup’. Kwalliyar fuskar Amare na kara fito da kyawun Amarya yayin da wasu kuma take kara musu muni musamman idan aka yi rashin sa’ar samun kkwararriya mai yi.

Sanin kowa ne cewa ita dai kwalliya a yanzu ta zama babbar sana’a ga masu yin ta musamman idan muka yi duba da yadda ake danka musu kudade masu yawan gaske a lokaci daya, yayin da kwalliyar take ficewa a rana guda wani sa’in ma a cikin awanni kadan.

Yin wannan kwalliyar ta fuska ga wasu matan ya zamar musu tamkar Farillah a kowanne lokacin yin wani shagali ko da kuwa ba ranar Aure ba, bare kuma a kai ga ranar auren. Ta yadda ko da Angon ba ya bukatar wannan kwalliya a kan fuskar Amaryarsa sai ya zama matsala, auren ma ya fara samun tangarda duk ta dalilin hana wannan kwalliya ‘Makeup’ da Ango ya yi. Yayin da wasu kuma sam! ba su damu da yinta ba ko da kuwa Angon ne ke son a yi musu.

Yin kwalliyar fuska ba za a kira shi haramun ba, sai dai wasu sukan canja mata kammani ta yadda in aka yi musu suke kaurace wa yin Sallah har sai bayan karewar shagalin ranar. Sanin kowa ne cewa ‘Ya mace an san ta gwanar Ado da kwalliya ce, sai dai ta wani fannin yin kwalliyar fuskar ‘Makeup’ idan ta yi yawa takan lalata fatar fuskar wadda aka yi wa ta hanyar yin amfani da wasu kayayyakin kwalliyar tare da daukar wasu kwayoyin cututtukan da ba a san da su ba musamman ga masu yawaita yin ta a koda yaushe. Mabiya Tsokacin Taskira sun bayyana ra’ayoyinsu a kan yin kwalliyar fuska ‘Makeup’, a game da amfaninta ko akasin haka, tare da bayar da shawarwari ga masu yi da kuma marasa yi. Ga dai bayanan nasu kamar haka:

 

Fadila Aliyu Musa daga Jihar Kano:             

Ai shi ‘makeup’ abu ne mai kyau musamman a gurin mata domin kuwa ita mace ai dama ‘yar kwalliya ce. Tabbas ina da bukata domin kuwa kowacce mace burinta ranar aurenta ayi mata ‘makeup’ na gani na fada saboda a wannan lokacin kowa kwalliyarta yake son ya gani. Yin ‘makeup’ yana da matukar amfani a wannan lokacin saboda tanan ne ake iya bambanta amarya da sauran matan da suke gurin bikin. Shawarata ga masu yin ‘makeup’ shi ne duk irin kwalliyar da za ki yi kada ki wuce gona da iri sannan a ki ya yi duk abinda ya sabawa addinin musulci, kuma kada ki ki yin sallah saboda kina tsoran kada ki goge ‘makeup’ dinki a kiyaye matuka da wannan domin kuwa sallah tana gaba da komai Allah ya sa mu dace Amin.

 

Ibrahim Danmulky daga Jihar Kano:

‘Makeup’ abu ne me kyau in dai ba a ketare inda shari’ar musulunci ta iyakance ba. Kwarai kuwa, ranar aurena ba laifi dan an yiwa amaryata ‘makeup’ amma ba irin ‘makeup’ din da zai sakata muni ba, dan gaskiya sau tari wasu ‘makeup’ din baya karbarsu, daga sune ko daga masu yin kwalliyar ne Allah masani. Daga cikin amfanin ‘makeup’ yana kara bambanta Amarya da sauran mata a ranar bikin. Masu yin ‘makeup’ a ranar biki shawarar da zan basu daya ce, su yi a hankali kar su tsawwala da yawa, abu ne na rana daya kuma kar su wuce gona da iri.

 

Zainab Muhammad (Zee Md), daga Jihar Kano:

Ra’ayina game da yiwa amarya ‘makeup’ shi ne zamani ne ya kawo mu haka, kuma hakan yanada kyau domin yana kara fitowa da amarya sosai a rana mafi muhimmanci a rayuwarta. Eh! idan akace ni ce amarya a yau zan so ayi min, dalilina shi ne saboda ranar aure ranar farin ciki ce kuma rana ce ta musamman da mutum ya kamata ya yi kyau kowa ya ganshi ya ce woww! masha Allah ‘bride’ ta fito, dalilina na biyu shi ne idan ba a yi ba, wasu za su rinka tunanin ko auren ne baka farin cikinsa kowani abu makamancin hakane ya sa kaki yi. Amfanin ‘makeup’ ga amarya shi ne zai taimaka wajan kara fiddo da martabar kyau da amaryar take da shi, sannan a duk inda aka ganta za a gane ita ce amaryar, rashin amfanin ‘makeup’ shi ne ya kan canza kamanni ko ma wani lokacin a maimakon ya karawa amaryar kyau sai ya rage mata shi. Shawarata ga masu yin ‘makeup’ ya yin aure shi ne su ci gaba da yi domin hakan yana da kyau amma ana yin dai-dai misali wadda ba za ta canzawa mutum kamanni ba. Shawarata ga marasa yin ‘makeup’ kuma shi ne su daure su rinka yi koda sun kasance basa yi su yi a lokacin aurensu.

 

Dakta Maryama ‘Yar Mutan Sakkwato:

A gaskiya ba ni da ra’ayin yin ‘makeup’. Gaskiya idan har yau a ka wayi gari aka ce ni ce Amarya bana bukatar ‘makeup’ din nan da ake yi a zamanin yanzu, kin san dalili? Dalilina shi ne shi wannan ‘makeup’ din sau tari akan yi wa mutum shi sai kiga ya koma wata halitta ta daban, da wanda zai yiwa ma’ana da akasin hakan. Gaskiya yin ‘makeup’ din da Amarya ba shi da amfani. Shawarata zuwa ga masu yin ‘makeup’ din aure su san abinda ya dace, ko da za kiyi ‘makeup’ din ayi na hankali kana idan har a kayi kar ace gaskiya na yi ‘makeup’ ba zan yi alwala ba ka da ‘makeup’ dina ya lalace, shikkenan fa ba za’a yi sallar ba, to dan Allah ina amfanin wannan lamarin?, ‘Yan matan Amarya dama ita kanta amarya dan Allah a nutsu ayi abinda ya dace.

 

Yusuf Yahaya Gumel:

A ganina babu laifin yi, idan har akwai damar hakan ina nufin dama ta kudi domin ana kashe kudade wajen yin. Za a iya yi, amma cikin tsarin cewa ba za a cika abubuwan ba, ta yadda kammaninta zai jirkita, a kuma kaucewa amfani da abin da zai cutar da fatarta. Amfanin yi yana karawa amare kyau, yana bayyanar da zahirin amarya kai tsaye saboda kwalliyar ta bambanta. Rashin Amfanin yi, A na kashe kudade sosai, wasu ko Sallah ba su yi, saboda kar su yi alwala su wanke. Idan a ka hadu da wadda ba ta iya ba, tana iya mayar da fuskar amaryar ta zama kamar dodanniya. Shawarar da zan bayar shi ne za a iya yi, yadda za ta yi kyau ba tare da an narka abubuwan ba da kammanin zai jirkita. Idan babu halin hakan a hakura. Idan mijin da za ki aura ba ya so, to ki hakura da yi zai fi.

 

Naja’atu Ali daga Maradi, kasar Nijer:

Ra’ayina game da yiwa amarya ‘makeup’, A gaskiya ni ina da ra’ayin haka, saboda zamani ne a lokacin baya da ‘makeup’s’ ba ta shigo ba babu wanda yake damuwa wai dan za a kai amarya ace dole sai an yi ‘makeup’, sai dai a zamanin baya suna yin tasu ta gargajiya. ‘Makeup’ yana da amfani sosai ga Amarya, sai dai kuma ba ko wacce/wanne suke so ba, wata tana so angon ne baya so, wani angon shi kuma yana so Amaryar ba ta Ra’ayi. ‘Makeup’ yana da amfani sosai, ko dan aje tarihin hotuna wanda komai jimawa za ki dauko hotunan auranki ki yi alfahari da irin kwanliyar da kika caba a wannan ranar. Abu na biyu, wani lokacin ko da Amarya ta sha sutura me tsada, to wallahi idan ba ta yi ‘makeup’ ba a banza ne, dan sai kin yi ‘makeup’ ne kin sha daurin dan kwali za ki fito. Shawarar da zan bawa masu yin ‘makeup’ ga auren su, abu ne me kyau ku ci gaba da yi bama sai ranar aure ba har gidan miji zai yi iya yi amma ba irin ‘makeup’ din nan me cika fuska ba ‘Simple,’ ma’ana sama-sama kar ta yi yawa.

 

Hassana Yahaya Iyayi (Maman noor), Jihar Kano:

Gaskiya a yiwa Amarya ‘makeup’ tana kyau sosai kuma hakan yana kayatarwa sosai barin ma a samu wadda ta kware abin yana bada citta. Amarya duk muninta za ki ga ta fito fes! abunta. Sosai zan zauna a rangada min abata dama ai mace ‘yar ado ce. Ni shawarata a ci gaba da ‘makeup’ Amarya da wadda ba Amarya ba a fito fes! uwar gida ma a cancare da kwaliya.

 

Sako daga Ayshat Humaira (Ayshe) Jihar Kano:

Ina fara gaida mijina abin alfaharina, sai ‘Yan uwana, Yayye da abokan arziki, Masoya Annabi Muhammad (S.A.W).

 

Sako daga Mansur Usman Sufi (Sarkin Marubutan Yaki):

Assalam alaikum warahamatullah Barka da Juma’a. Ina mika sakon Barka Da Juma’a ga abokina Ahmad Hassan (Dogo) da kuma taya murnar Aurensa da aka yi, fatan Allah ya bada zaman lafiya, ina yabawa kungiyar Shabbabu-khairi bisa gudunmowar su a wannan biki, irin su Usman Soja, Mustapha Captain, Habu Sanyi, Mubarak fada, Nura,Yusuf Boso, Isah Usman, Kasiwini Usman, Abba Mada, Abdul (kafisi), da dukkan sauran ‘Yan kungiyar shabbabu, da basu samu damar ganin sunan su ba ina yi muku Barka da juma’a.

 

Sako daga Abdulazeez Shehu (Yarima Shaheed) 08037675021:

Ina gaida abokina Imaran Muhammad tare da Yarima Sameer, ina gaida gimbiya sarautar mata Gimbiya Shahida, ina gaida dukkan ma’aikatan Razeez Online Tb.

Exit mobile version