Connect with us

MATASAN ZAMANI

Amfani Da ‘Social Media’: Matasa Mu San Cewa Mutunci Madara Ne…

Published

on

Matasa na gida da waje barkanmu da sake haduwa da ku a filin naku mai farin jini na Matasan Zamani. Idan ba a manta ba, a makwanni biyu da suka gabata, mun tattauna a kan batun kafafen sadarwa na zamani da jama’a suke amfani da su domin walwala da sada zumunci. To har yanzu dai muna nan a kan wannan batu na wadannan kafafen.
A wannan makon, zan yi jan hankali ne ga matasa game da mu’amalarsu a wadannan sabbin kafafen sadarwa na zamani (Social Media). A kullum ina fada cewar (Social Media) kafofi ne wadanda matasa za su yi amfani da su wajen gudanar da kasuwanci domin cigaban rayuwarsu da ta al’ummarsu. Ba wurare ne da ya kamata matasa su yi amfani da su wajen cin zarafin junansu ko taba mutunci da darajar manyan mutane wadanda su ka fi su shekaru da sanin rayuwa ba.

Dan haka akwai bukatar matasa su cigaba da tsaftace yanayin yadda su ke mu’amala da wadannan kafofin sadarwa na zamani domin ganin sun tsaftacce ayyukansu sun kuma maida hankali wajen ganin sun yi amfani da kafofin wajen kasuwanci da samun kudi kamar yadda tuni takwarorinmu ‘yan Kudu sun yi mana nisa sosai ta wannan fuska.

Sannan kuma matasa su kasance masu wanzar da siyasa mai tsafta ta mutuntawa da girmama juna ko saboda rayuwarsu ta gaba. Kowane dan adam Allah ya yi masa matsayi da daraja a rayuwa, idan ka dauki sabbin kafafen sadarwa na zamani a matsayin wuraren batanci da cin zarafin al’umma ba ka san yadda rayuwa za ta kasance ba a gaba. Kila ya kasance wanda ka ci zarafinsa ko mutuncinsa Allah ya yi masa wata ni’ima wacce ka ke bukatar taimakonsa wanda daga karshe sai dai ka ji kunya ko samun sakamakon rashin bukata sakamakon cin zarafi da batanci ga mutane.

In ma ba wannan ba kila a siyasar taka wata dama ta taso a ce ka da a baka saboda ba ka ganin girma da mutuncin mutane. Dan haka ina kira ga ‘yan uwana matasa da a kara sanya lura da kulawa a tsaftace kalamai a zauna lafiya da jama’a cikin girmamawa da mutuntawa saboda gaba.

Rayuwa da siyasa su na bukatar mutunta al’umma da zaman lafiya da mutane da kuma ganin girmansu. Wadannan sinadarai ne na mu’amala da zamantakewa wadanda su ke taimakawa Dan Adam ya kai ga samun cigaba da wani matsayi a rayuwarsa ba tare da ya yi tunanin hakan ba. Dan haka matasa a kiyaye da batanci da labaran karya da cin zarafi da kalaman kiyayya da batanci a kafafen sadarwa na zamani a zauna lafiya da al’umma za a ga amfanin hakan a rayuwa.

Advertisement

labarai