Amfani Da Wayar Hannu Yayin Tuki Na Kara Cin Rayukan Mutane, In Ji FRSC

Daga Mahdi M. Muhammad, Abuja

Hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC), ta ce, amfani da wayar hannu yayin tuki na da matukar hadari kuma zai iya sanya rayuwar wasu masu amfani da hanyar cikin hadari.

Bamidele Ayanwale, kwamandan sashin FRSC a Oraifite, karamar hukumar Ekwusigo a Anambra, ya yi wannan maganar ne lokacin da yake gabatar da lacca a jami’ar Nnamdi Azikiwe (NAU) da ke Awka, a ranar Talata.

Sashen addini da hulda da jama’a na kwalejin fasaha ne suka shirya shirin don karrama daliban shekarar karshe.

Ayanwale, wanda Chinedu Okonkwo daga Oraifite Command ya wakilta, ya ce, dokar kafa hukumar FRSC ta 2007, Sashe na 10 (4), ta hana amfani da wayoyi yayin tuki saboda wasu dalilai.

A cewarsa, an gano amfani da wayoyi yayin tuki na daya daga cikin abubuwan da ke haifar da hadarurruka, raunuka da kuma mace-mace a cikin ‘yan kwanakin nan.

“Babu wani sako ko kira da yake da muhimmanci kamar rayuwarka, kuma abin da hakan ke nufi shi ne duk sakonni ko kira na iya jira. Sau da yawa direbobi da mutane marasa laifi suna mutuwa saboda shagala daga amfani da wayoyi yayin tuki,” in ji shi.

Ya kara da cewa, “Idan ka ga kira ko sako yayin da kake tuki, abin da ya fi kyau ka yi shi ne ka sauka gefen titi lami lafiya ka amsa kiran idan ka ji yana da matukar muhimmanci. Idan ba ka tsaya don amsa wannan kiran ba, za ka shagala. Kana iya kallon wani wuri wanda kuma hakan na uya haifar da hadari ga wasu motocin ko bugun masu tafiya.”

“Amfani da wayoyin hannu yayin tuki ya kasance babban abin damuwa ga aminci a kan titunan Nijeriya wanda hakan ne ya sa muke ba masu ababen hawa umarnin yin biyayya ga jami’an FRSC da dokokin hanya da ka’idojin zirga-zirga a kowane lokaci,” in ji Ayanwale.

Jami’in kiyaye hadurran ya kuma bukaci masu ababen hawa da su guji saurin gudu da shan barasa yayin tuki, yana mai bayyana cewa, wadannan su ne dalilan da ke haifar da hatsarin hanya.

Ya yi kira ga daliban da ke fita da su zama masu sauya canji da kuma jakadun kiyaye hadurra a cikin garuruwansu ta hanyar isar da sakon ga jama’a.

A nasa jawabin, Dakta Anayo Ossai, mai ba da shawara ga ma’aikatan sashen, ya shawarci daliban da ke shirin su yi amfani da horon da suka samu daga makarantar su zama masu dogaro da kansu da kuma dogaro da kai.

“Babu lokacin yin kasala da zama ba tare da aikin yi ba, tare da iliminka da iliminki, kun sami karin kwarewa don zama masu amfani ga kanku da kuma al’umma,” in ji Ossai.

Shirin ya gabatar da bikin karramawa inda aka karrama Ayanwale, saboda kwazonsa na tabbatar da tsaro a hanyoyin Anambra.

Exit mobile version