Amfani Ilimin Muhalli Da Wayar  Da Kai A Arewacin Nijeriya

Tare da Umar Saleh Anka usanka01@gmail.com      08036005151

Duk wata hanya da dan’adam zai bi wajen warware wasu matsaloli da suka shafi muahhli, da kuma samar da waraka ta hanyar inganta muhalli. Wanda a sakamakon  hakan ne jama’a ka iya samun wata dama ta yanke shawara yadda za a iya kula da muhalli. Babu wani gari ko birni ko kauye da zai samu ci gaba ,ba tare da samun kyakkyawan ilimi a kan muhalli da suke zaune ba. Wannan yana nuna cewa idan muka zauna kara-zube a muhallinmu ba tare da samun ingantaccen ilimi a kan meke faruwa da mu a kusa da kuma nesa da mu ba. Ya zama wajibi gare mu mu san meke faruwa da muhallinmu a yau da gobe. Akwai karancin wayewa a Arewacin Nijeriya ta fuskar sanin ilimin muhalli a tsakanin jam’ar gari . A sakamakon haka gwamnatoci da kungiyoyin sa-kai sai sun tashi tsaye wajen wayar da kan ‘yan Arewa kan ilimin muhalli da illolin da ke tattare da gurbatar muhalli, ta haka ne za a samu kyakkyawa da kuma ingantaccen mutsuguni.

Wasu daga cikin manyan kalubale da ke damun Arewacin Nijeriya.

Rashin masaniya a kan muhalli na da babban tasiri a kan ingantacciya rayuwa dan’adam, saboda haka babu wani guri ko al’umma da za ta ci gaba ba tare da ta inganta muhalli ba. Ya zama dole mu canza tunaninmu da halin ko-in-kula da muke da shi domin samun ingantacciyar rayuwa. Domin in har muka zauna kara-zube, to muna tare da tabewa, da kamuwa da cututtuka da bakinciki da kuncin rayuwa.

Kawo Dauki: Dolene gwanonin Arewa su farka daga gyangyadi domin su hada karfi da karfe wajen sanar da al’ummarsu illolin da ke tattare da rashin sanin yadda jama’a za su kula da muhalli domin samun ingantacciyyar rayuwa domin yawancin cututtuka da ke addabarmu na samuwa ne saboda halayyar dan’adam a kan muhallinsa.

Akwai hanyoyi da dama da gwamnatocin Areawa za su bi wajen ilimantar da jama’arsu domin samun kyakkyawan muhalli da ingantacciyar rayuwa musamman  wajen kula da gandun daji da burtali da har da ma gasar noma a tsakanin kananan yara da samari da ‘yanmata  kai har ma da tsofaffi domin samun ci gaba ta bangaren rayuwa da lafiyar dan’adam.

Kafa Kungiyoyin Kula Da Muhalli :  Lallai kafa kungiyoyin kula da muhalli a makarantun firamare da sakandare da kuma makarantun gaba da sakandare zai taimaka wajen canza tunanin yara tun daga matakin farko domin samun ingantacciyya rayuwa, hakan zai sanya yara su taso da akidar son kula da muhalli cikin sauki. Haka zai bada dama wajen koya musu yadda za su dasa bishiya da kula da ita domin kare muhalli daga zaizayar kasa da sauran hanyoyin kula da muhalli.

Bada Horo Ga ‘Yan jarida : Gidajen jaridu na bugawa da sauransu na da matukar rawa da za su taka wajen ci gaban ilimi, duk da cewa gidajen jaridu na da shafuka na musamman domin wayar da kan jama’a a kan muhalli, amma za ka ga cewa ba sa bada ingantaccen ilimi saboda masu kawo rahotonnin ba su da ilimin muhalli. Saboda haka samar da hanya ta horar da ‘yan jarida zai taimaka wajen samun bayanai ingantattu a kan kula da muhalli.

Ilimantar Da Mata kan Yadda Za A Kare Muhalli: Ilimin mata na da muhimmanci ga daukacin al’umma domin su ne suke amfani da makamashi, su ne suke fara fitar da shara , kuma su ne masu rainon yara saboda haka yana da muhimmanci a sanar da su illolin da ke tattare da gurbacewar muhalli, domin kuwa sanar da su zai bada dama su koyawa yara yadda za su kula da kansu da da kuma muhallin da suke ciki ba tare da wata wahala ba. Suna da muhimmiya rawa da za su taka wajen kula da muhalli. Wannan ne dalilin da ya sa  ya zama dole gwamnatoci na tarayya, jahohi da kuma kananan hukumomi su ba wa mata horo na musamman a kan kula da muhalli.

Da wannan ne muke ba da sharawa ga gwamnonin Arewa da su ba wa kula da muhalli muhimmanci don samun ingantacciyar rayuwa ta hanyar ilimantar da jama’armu illolin da ke tattare da rashin muhalli nagari.

Exit mobile version