Connect with us

KIWON LAFIYA

Amfanin Azumi A Jikin Mutum (2)

Published

on

Azumi ke dakile hayayyafar kwayoyin halittar cutar daji, da kuma hana su cin abinci; kunga kenan zasu dinga mutuwa a hankali. Duk da cewa ba a gama gano cikakkiyar amsar da yasa azumi ke yaki da cutar kansa ba, masana suna fatan samun gamsassun bayanai domin gano bakin zaren.

Azumi na taimakawa kwayoyin halittun jikin mu wajen jurewa da hana su gazawa ga barin saurin tsufa. Wato jikin mutum yana gudanar da ayyuka masu taarin yawa a duk dakika guda.

Wasu masana sun kiyasta cewa : a kwayar halitta daya, ana gudanar da ayyukan da suke tallafar rayuwa dai-dai har tiriliyan guda! Ka ji ikon Sarki mai iya halitta!

Saboda haka, wadannan ayyuka sun isa su gajiyar da kwayar halitta. Kun san yau da gobe ta ki wasa. To azumi yana rage yawan wannan ayyuka saboda kwayoyin halittar jikin mu su huta, ta haka ba za su yi saurin tsufa ba.

Azumi ya na washe kwakwalwa ta hanyar zubo da wani sinadari (BNDF). Kuma azumi ya na koyawa kwakwalwa juriya da kau da kai ga barin ci, sha, da jima’i, wadanda yawan yin su na kawo wa jiki rashin lafiya. Saboda haka kwakwalwa ta na adana yadda ta ke yin wannan juriya a ma’adanar tara bayani wato memory. Shi yasa duk inda a ka ce A ka yi azumi bakwai, kwakwalwar zata fara mantawa da batun abincin rana.

Azumi na bawa tsokar jiki ‘yanci da zata sakata ta wala. Dalilin hakan kuwa shine: kitsen da ake samu ya lullube tsokar naman jiki a sassa daban daban yana zama makamashin konawa domin samar wa jiki kuzari. Karancin kitsen kan iya sa tsokar ta kara karfi da kuma samun sararin da zata waala.

Ga wani sirrin gyaran fata na musamman da hana tsufan ta da wuri. Fatar jiki tana da wani sinadari da yake tallafa mata, ya gyara ta, ya kula da karkon ta; ana kiransa da “collagen”. Amma sikarin “glucose” da yake a jikin mu yana sauya wa “collagen” yanayi, da rage masa karfi. To, tun da azumi yana kone mafi yawan sikarin jiki, kenan sinadarin “collagen” zai dinga gudanar da aikin sa na gyaran fata ba tare da katsalandan ba.

Karin bayani kadan akan “collagen”. Shine abinda Sarkin halitta ya sanya mana a fatar mu, kashin mu, kashe kara, da sauran gurare domin ya zamo mai tallafi a wajen da ya kasance. Abin da ke kawo yamushewar fata yayin da tsufa ya cimma dan adam, shine raguwar yawan “collagen” a fata.

Azumi na kara lafiyar zuciya. Binciken masana ya gano cewa yin azumi yana da alaka da ingarmar tsokar zuciya, da karuwar girman hanyoyi jini da suke jikin zuciya; wato tunda sun kara girma, jini zai wuce ta cikin su ba tare da wata matsala ba.

Haka kuma akwai man kwalasturol (cholesterol) da jiki ke konawa yayi azumi. Shi wannan mai na “cholesterol” yana son zama ya taru a hanyoyin wucewar jini, idan yayi yawa ma, yakan hana wucewar jini wanda hakan kan iya jefa zuciya ko kuma gabar da aka toshewa jinin cikin matsala.

Ana nan ana bincike akan alakar azumi da saurin warkewar ciwo. Babu isassun bayanai game da hakan, amma masana sun yarda cewa: akwai yiyuwar cewa; azumi zai iya taka muhimmiyar rawa wajen warkewar ciwo.

Kamar yadda a addinance; azumi garkuwa ne daga wuta, haka a duniyance, azumi garkuwa ne daga cututtuka. Bayan tokarewa da hana shigowar kwayoyin cuta cikin jiki, azumi na karfafa garkuwar jiki domin ta yaki sauran cututtuka da suka riga suka shigo.

Daya daga cikin dalilan da yasa garkuwar jiki ke samun karfin gwiwa wajen yakar cututtuka shine: yawan aikin da kwayoyin halittu keyi yana raguwa lokacin azumi. Wannan zai basu rarar lokaci da hutawa ta yadda zasu iya shagala da yakar cuta, a madadin ace suna gudanar da wasu ayyukan.

Haka kuma azumi yana rage hauhawar jini na wani dan lokaci. Ta yaya hakan ke faruwa? Ta hanyoyi guda biyu. Da farko dai tun da mutum ba zai ci abinci ba tsawon lokaci, to hakika ya rage shigar gishiri da mukeci a abinci cikin jiki.(shi gishiri yana kara hauhawar jini).

Hanya ta biyu ita ce fitar gishiri daga jiki ta hanyar bawali, da gumi (ziffa). Saboda kasancewar gishiri a cikin jini ya na jawo shigar ruwa da yawa cikin hanyoyin jini, hakan kuwa ke kara yawan jini har ya hauhawa.

Ya na daga hanyoyin da azumi kan kawo karuwar lafiya a jiki: karuwar ruwan jiki. Saboda na fada a baya cewa azumi yana kone kitse da maiko masu taruwa a jiki. Shi wannan ruwan jiki, a cikin kwayoyin halittun jikin mu suke wanka, musayar sako, musayar sinadarai, da sauran su.

A takaice, azumi na da dumbin alfanu a jikin mu. Yana wanke datti da kwayoyin cutar dake bututun ciki, Yana tsafftace jini da hanyoyin sa, Yana gina kwayoyin halittar kwakwalwa da hana su tsufa da wuri da kuma kare su daga cututtuka, yana gyara fata hana ta tsufa da sauri, yana washe kwakwalwa da kaifafa tunani da sanya juriya da dauriya wajen kula da kawunan mu yayin sha’awa ta ci da sha da saduwa.

Ya na kone kitse da maiko domin kwayoyin halittun jikin mu su samu wadataccen ruwan da ke basu damar gudanar da ayyukan su. Sannan yana yiwa kwayoyin halitta garan bawul.

Ya mai karatu, wannan kadan kenan daga cikin abin da zan iya kawowa kuma kadan ne daga abin da masana yadda jikin dan adam ke aiki suka fara gaanowa. Tabbas nan gaba, za’a gano wasu fa’idojin azumi a jikin dan adam.

Mai karatu, a sha ruwa lafiya. Allah Ya kaimu wani makon. Ameen.

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: