Yusuf Shuaibu" />

Amfanin Ganyen Mangwaro A Jikin Dan’adam

Ko kun san cewa masana ilimin kimiyyar magunguna, na kasar Sin da Indiya, sun tabbatar da cewar daya daga cikin manyan magungunan warkar da ciwon suga (diabetes) shi ne Ganyen Mangwaro?

Ganyen Mangwaro na dauke da sinadarai masu yawan gaske da ke amfani a jikin dan’adam, amma kash, mutane da dama ba su san hakan ba!

Yadda ake amfani da shi a matsayin maganin ciwon Suga

(1) A tsinko ganyan Mangwaro,masu kyau. A wanke su sosai

(2) A sanya ruwa a murhu, a tafasa shi, har na tsawon minti biyar ba tare da ganyen ba.

(3) Sai a zuba ganyen a cikin ruwan zafin da ke kan murhu, tare da Man Zaitun. A bar shi ya yi ta tafasa, har na tsawon minti biyar zuwa goma.

(4) Sai a sauke shi a tace.

(5) Sai a sanya shi cikin kwano ko gilashi mai kyau, a bar shi ya kwana

(6) Sai a sha wannan ruwan da sassafe bayan an tashi daga barci, kafin ka ci komai.

Wannan maganin, yana kawar da abubuwa (marasa kyau masu guba) daga jikin mutum, kuma yana rage yawan suga da ke cikin jini. Haka kuma yana saukar da hawan jini sosai.

Asma,Tari, Ko Matsalar Numfashi

Yakan sa a samu numfashi mai kyau,kuma cikin sauki,da yardar Allah.

Yawan Fargaba, Zaman Dar-Dar Ko Rashin Nutsuwa:

Idan aka zuba cokali biyu zuwa uku, a cikin ruwan wanka, sannan a yi wanka da shi. Yana sanya a ji jiki garau, kuma a ji hankali ya kwanta,da yardar Allah.

Dutsen Dake Zama Cikin Hanta,Madata Ko Koda.

Mai wannan ciwon, zai busar da ganyen Mangwaro (a inuwa), sannan ya daka shi. A zuba garin a cikin kofi/glass ko kwano, a bar shi ya kwana. A rinka sha kullum da safe. Wannan yana narkar da dutsen da ke jikin koda sosai

Ciwon Tari,Gushewar Murya Ko Asthma

A dafa ganyen Mangwaro, a sanya masa Zuma (kadan). Yana taimakawa kwarai da gaske cikin sauri

Amfanin Bagaruwa A jikin Dan’adam

Bagaruwa na da sirrori masu yawa, sannan kuma tana da amfani wajen samar da waraka da kare lafiyar dan’adam. Ga amfanin da yake yi a jikin mutum.

1. Bagaruwa na maganin tsutsar ciki. 2. Itacen bagaruwa na maganin gudawa mai tsanani. 3. Yana kuma kawar da matsalar zubar jini. 4. Bagaruwa na maganin ciwon hakori: Ana daka ‘ya’yan Bagaruwa a riga zubawa ko kuma a samu ‘ya ‘yanta wadanda ba su bushe ba a rika matsa ruwanta a cikin wurin. 5. Bagaruwa na maganin ciwon sikari wato ‘Diabetes’. 6. Bagaruwa na kawar da warin jiki da warin baki. 7. Yana magani da hana kamuwa da cutar sanyi musamman a jikin mata.

Exit mobile version