Amfanin Hulba 21 Ga Lafiyar Dan’adam
  • English
  • Business News
Wednesday, October 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Amfanin Hulba 21 Ga Lafiyar Dan’adam

bySani Anwar
1 year ago
Hulba

Kamar yadda muka sani, Hulba kalma ce ta larabci; da harshen turanci kuwa, ana kiran ta da ‘Fenugreek’. Hulba wani tsiro ne mai matukar amfani ga lafiyarmu, sannan mutane sun kwashi shekara da shekaru suna amfani da shi; domin samun waraka daga wasu matsaloli da suka shafi lafiyarsu.

Mutane na amfani da ganye da kuma kwayar hulba wajen samar da magunguna shekaru aru-aru. Hulba ta yi matukar shahara a kasashe da dama na duniya, sai dai an fi samun ta a wasu daga cikin kasashen Larabawa, musamman Kasashen Misra, Sin da kuma Indiya.

  • Amfanin Namijin Goro 16 Ga Lafiyar Dan’adam
  • Ko Kin San… Sirrin Hulba Ga Mace?

A Kasar Indiya, ana kiran ta da ‘Methi’; wato a yaren Hindu, a yaren Telugu na Indiyan kuwa, ana kiran ta da ‘Menthulu’. Wani bincike da wata kafar yada labarai ta yanar gizo ta wallafa ya nuna cewa, Hulba ta shahara a Kasar Indiya; sakamakon irin amfanin da take da shi ga lafiyar Dan’adam, ta yadda za a iya kiran ta da cewa, gidan kowa akwai.

A al’adance, mutanen Kasar Indiya; na amfani da kwayar Hulba a matsayin wani mahadin samar da magunguna, baya ga amfanin da suke yi da ita, don samar da wasu hade-hade na inganta lafiyar jiki da kuma yadda suke amfani da Hulbar, domin kula da lafiyar gashi.

Sai dai, binciken zamani na kwanan nan da masana suka gudanar a kan Hulbar ya nuna cewa, za ta iya samar da magunguna da hade-haden inganta lafiya fiye da yadda aka sani a baya.

Har ila yau, daga cikin amfanin Hulba ga lafiyar Dan’adam da masanan suka gano, har da taimaka wa masu ciwon siga, ciwon ido, gyaran gashi da kuma fata. Hakanan, ana amfani da Hulba kan matsalar basir, matsalolin ciki da sauran makamantansu.

Bayanai Daki-daki Kan Amfanin Hulba Ga Lafiyarmu:

1- Hulba na hana bushewar fata: Bincike ya tabbatar da cewa, amfani da Hulba na hana bushewar fata. Saboda haka, duk mai fama da wannan matsala ta bushewar fata; zai iya amfani da hulba don yin maganin wannan matsala.

Yadda za a yi shi ne, a samu garin hulba a kwaba da ruwa, amma kwabin ya yi kauri, sai a shafa a fuska, a bar shi har zuwa tsawon rabin awa, daga bisani sai a wanke.

2- Hulba na maganin basir: Ga mutanen da ke fama da wannan matsala ta basir, za su iya amfani da hulba; su kuma samu sauki cikin yardar Ubangiji. Za a samu hulba a dafa, sai a sauke; bayan ta huce sai a zuba zuma a ciki, a rika sha awa guda kafin a kwanta barci.

3- Hulba na maganin rashin ruwan nono ga mai shayarwa: A wasu lokutan, a kan samu mace ta haihu; amma sai ta samu karancin nono. Yin amfani da hulba zai samar wa da mai shayarwa ruwan nono, sannan kuma zai taimaka wajen girman jaririnta.

A kasashen da ke Nahiyar Asiya, mata kan yi amfani da hulba domin yin maganin matsalar rashin ruwan nono ga mai shayarwa. Masana sun ce, hulba na taimakawa wajen samar da ruwan nono ga mata masu shayarwa ne, sakamakon wani sinadari mai suna ‘phytoestrogen’ da ke kunshe da shi. Ana samun wannan fa’ida ta hulba ne; ta hanyar shan ta a cikin ruwan shayi.

Ko kuma mace ta samu ‘ya’yan hulba ta dafa da man Ridi ta rika ci har tsawon kwana uku, sannan ta rika shafa man hulbar a nonon nata, da yardarm Allah za a samu biyan bukata. Domin kuwa, za ta samu ruwan nonon da zai wadatar da jaririnta, ya kuma kasance cikin koshin lafiya.

4- Amfani da hulba na rage ‘kwalastaral’ (kitse marar kyau) a cikin jini; bincike ya tabbatar cewa, yawan amfani da hulba na taimakawa wajen rage yawan kwalastaral a cikin jini, musamman marar amfani da ake kira ‘bad cholesterol’ ko kuma LDL’ a turance.

Akwai Ci gaba a mako mai zuwa cikin yardar Allah

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki
Labarai

ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

October 8, 2025
Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu
Labarai

Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

October 8, 2025
Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung
Manyan Labarai

Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

October 8, 2025
Next Post
Daliban Nijeriya 6 Sun Lashe Gasar Gwanayen Koyo Ta Cambridge

Daliban Nijeriya 6 Sun Lashe Gasar Gwanayen Koyo Ta Cambridge

LABARAI MASU NASABA

ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

October 8, 2025
Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

October 8, 2025
Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

October 8, 2025
A Kama Wani Likitan Bogi A Neja

‘Yansanda Sun Kama Masu Laifi 153, Sun Ƙwato Miyagun Ƙwayoyi A Jihar Jigawa

October 8, 2025
An Fara Biyan Ma’aikata Sabon Mafi Ƙarancin Albashin N70,000 A Borno

‘Yansanda Da Mutanen Gari Sun Daƙile Harin Boko Haram A Borno

October 8, 2025
…ACF Ta Nesanta Kanta Da Goyon Bayan Akpabio

‘Yan Nijeriya Sama Da Miliyan 33 Ne Ke Fama Da Matsananciyar Yunwa – Akpabio

October 8, 2025
Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

October 7, 2025
Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

October 7, 2025
Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

October 7, 2025
Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

October 7, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Exit mobile version