yusuf" />

Amfanin Man Tafarnuwa A Jikin Dan’adam

Tafarnuwa tana daga cikin tsirrai wadanda duniya ta dade tana amfana da su. Annabi (S.A.W) ya tabbatar da cewa tana da amfani sai dai ba ya cinta saboda dalilin warin da take da shi.

-Ciwon Daji (CANCER): Duk mutumin da yake fama da ciwon daji ya yawaita amfani da tafarnuwa. Idan ciwon dajin a kan fatar jikinsa ne, sai ya rika shafawa a jikinsa bayan ya sha cokali guda tare da zuma. Idan kuma sankaran mama ne (Breast Cancer) wanda mata suke fama da shi, to duk matar da take fama da wannan ciwon ta rika yawan yin girki da tafarnuwa. Sannan ta rika shan tafarnuwar wacce aka gauraya tare da man habbah, kuma tana shafawa a jikin maman. In sha Allahu za ta warke.

– Basur : Duk wanda basur yake damunsa, ko yana shan wahala wajen fitar bayan gida, ko kuma masu yin bayan gida da jini, ko masu fama da kumburin ciki, ko kaikayin dubura, ga wani albishir gare ku : Ka je ka samo tafarnuwar mai kyau. (kamar guda biyu ko uku manya) ka cire bawon sannan ka bayar a da ka maka fura da ita. Ka samu nono mai kyau ka sha wannan furar da shi. In sha Allahu a wannan ranar ko washegari duk za ka fitar da basur din da ke cikinka. Kuma za ka samu lafiya da izinin Allah. Sannan ka rika gauraya man tafarnuwar tare da zuma kana sha kullum da safe. In sha Allahu kai da basur kun yi sallama.

– Sanyi Ko Kumburin Jiki: Duk mutumin da sanyi ya kumbura shi, ko kuma sanyin ya ratsa shi, kullum hancinsa ba ya rabuwa da majina, shi ma ga albishir : Ka samo Ganyen na’a-na’a ka dafa tare da citta. Sannan ka zuba man tafarnuwa cokali guda a ciki, ka sanya zuma sai ka shanye. Haka za ka rika yi har sati guda zuwa kwanaki 10. Kuma kana shafa man tafarnuwar a jikinka, In Allah ya yarda jikinka zai sabe, sanyin zai fita, kuma za ka warke.

– Sanyin Kashi: Masu fama da sanyin kashi ko kuma rikewar gabobi ga na ku : Ku samu man tafarnuwa mai kyau, ku gauraya shi da man habbatussauda. Sannan a dora shi bisa wuta mai ci a hanakali. Idan ya yi kamar minti biyar sai a sauke. Wannan man mai dumi za a rika shafawa a jikin kafar, ko baya ko kwankwaso, ko kafar da take ciwon. In sha Allahu ko da ciwon bayan ya fi shekara goma ana fama, to za a samu lafiya da izinin Allah.

– Hawan Jini Da Ciwon Zuciya : Bincike ya tabbatar da cewa tafarnuwa tana narkar da mummunar kitsen nan na ‘Cholesterol’ wanda shi ne yake toshe kofofin zuciyar Dan’adam, har ake samun hawan jini ko ciwon zuciya. To tafarnuwa tana narkar da shi kuma tana bude duk hanyoyin da suka toshe din. Sannan tana tsaftace jinin jikin Dan’adam. Ana so masu fama da hawan jini su yi wannan hadin domin samun kuzari da lafiya : A samu ganyen zogale danye a dafa shi tare da tafarnuwa. Bayan an tace shi kafin a sha sai a sanya man zaitun cokali guda, a sanya zuma sannan a sha. Kuma a yawaita cin ta a cikin abincin yau da kullum. In sha Allahu za a dace.

– Zazzabin Hanji (Typhoid Feber) Da Kuma Ulcer: Duk masu fama da wannan larurar ga magani nan da yardar Allah : Ka rika shan cokali guda na tafarnuwa gauraye da zuma kullum da safe, minti 30 kafin ka ci komi. In sha Allahu wannan zai kashe duk kwayoyin cutar da ke cikin cikinka. Haka nan masu macijin ciki ko tsutsar ciki su ma tsutsotsin za su mutu. Haka nan masu fama da gyambon ciki (Ulcer) su ma za su samu saukinta idan suka bi wannan hanyar. Kuma su rika sanya cokali guda na man tafarnuwar a cikin dukkan abincin da za su ci. Ko kuma a rika dafa abincin tare da ita.

– Ciwon Hanta: Tafarnuwa tana bama hantar Dan’adam kariya daga cututtuka. Kuma amfani da ita yana hana kitsen nan na ‘cholesterol’ taruwa ko ginuwa a jikin hanta, ballantana har a samu matsalar ciwon ciki ko kumburin hanta. Masu ciwon hanta su rika shan man tafarnuwa ko garinta wanda aka cakuda da zuma. In sha Allahu za a ga abun mamaki wato samun lafiya cikin kankanin lokaci.

Exit mobile version