Amfanin Ma’ul Wardi (Ruwan Fure) A Jikin Dan’adam

Ma’ul Wardi ana samar da shi ne ta hanyar matse ruwan da ke cikin wasu furen itatuwa, kamar yadda sunansa ya nuna, “Ma’ul Wardi” wato “Ruwan Fure” da Hausa ko kuma “Rose Water” a Turance.

Wannan sinadari na da matukar amfani ga lafiyar Dan’adam. Kadan daga ciki su ne:-

– Gyaran fata: Daga cikin manya-manyan amfanin Ma’ul wardi shi ne, yana gyara fata, saboda yana dauke da sinadaran ‘anti-inflamatory’wadanda ke taimakawa wajen gyara matsalolin fata, na ciki da kuma na waje. Abin sha’awa shi ne, ko da Aljani ne ya batawa mutum fatarsa, to Ma’ul Wardi yana gyara ta, idan aka hada shi da Ma’ul Khal da kuma sinadarin nan mai sanyi wanda ake hada turare da shi wato Alcohol ana shafawa. Likitoci sun ce, haka kawai ma ana iya shafa Ma’ul Wardi a fata, domin kyautata kyawunta da lafiyarta.

– Gyara Makogwaro: Shan Ma’ul Wardi, adadin da ya kamata, yana gyara makogwaro, yana sakin murya. Saboda haka Ma’ul Wardi yana da kyau wajen sha.

– Maganin Infection/Sanyin Mata.

– Kyautata lafiyar ido: Amma wadannan biyun ya kamata a nemin shawarar masana a kan yadda ake amfani da shi.

– Hana lalacewar abinci ko magani. Ma’ul Wardi yana dauke da sinadarin antiodidants, wanda ya ke hana abinci ko kuma maganin saurin rubewa ko lalacewa.

– Maganin Rauni, Kuna ko Yankewa: Ma’ul Wardi yana dauke da sinadaran Antiseptic da Antibacterial wadanda ke taimaka wa ciwo saurin warkewa. Wadannan sinadarai suna kuma taimakawa wajen yakar cututtukan da kan iya shiga yayin da aka samu rauni ko aka kone, sannan su taimakawa ciwon ya warke da wuri.

– Maganin Ciwon Kai: Ma’ul Wardi yana taimakawa wajen rage radadin ciwon kai ko ya warkar da shi gaba daya, idan aka shafa. Amma zai fi kyau a jika wani yanki mai kyau a cikin Ma’ul Wardi din, sannan a dora a kan tsawon na tsawan mintunan kamar 45.

– Maganin Hana Tsufa: Ma’ana Ma’ul Wardi na boye tsufan mutum, musamman yadda ya ke gyara fata da kuma kyautata lafiyar jiki da gyara idanu, idan ana amfani da shi yadda ya kamata bisa shawarar masana, to zai sa a daina ganin tsufar mutum.

– Cushewar Ciki/Rashin Cin Abinci: Ko a shekarar 2008, binciken likitoci ya tabbatar da cewa, Ma’ul Wardi na taimakawa wajen saukaka narkewar abinci a cikin mutum tare da warware hanji.

– Ma’ul Wardi yana da kyau wajen hada magungunan warware sihiri da lalata sharrin Aljanu. Yawanci dai an fi wanke rubutu da shi ko kuma a yi tofi a cikinsa.

Yadda Ake Amfani Da Ma’ul Wardi

– Za ka iya shafa Ma’ul Wardi a fatarka zallansa ko ka haDa shi da ruwa.

– Za aka iya zuba Ma’ul wardi a shayi ko lemo ko ruwa ka sha, hakan zai fi kyau, fiye da shansa kai tsaye.

– Likitoci ba su yi bayanin wata illa wajen shan Ma’ul Wardi ba, haka nan ba su ware wadanda ba za su iya amfani da shi ba, amma dai a shawarce, kada ka sha Ma’ul wardi sama da cokali biyu a rana daya.

– Za ki iya samun auduga mai kyau, sai ka dinga dangwalar Ma’ul Wardi kana goge fuskarki da shi.

– Za ki iya dura Ma’ul Wardi a cikin abin fesawa wato ‘sprayer’, sai ka dinga fesawa a jikinka idan ka yi wanka.

Exit mobile version