Ingantaccen muhalli na daya daga cikin matakan farko na ingantacciya rayuwa domin zubar da shara a ko ina na haddasa asara ta rayuka da dukiyoyin jama’a ba tare da samun mayar da wasu abubuwan da aka rasa ba.
Asara komai kankantarta ba ta da dadi, yawanci abubuwan da ke zama matsala sakamakon zubar da shara barkatai sun hada da ambaliyar ruwa daga kogi ko hanyoyin ruwan sama. Al’umma kan zuba shara cikin magudanan ruwan sama domin samun taki ko kuma zubar da shara don son zuciya, ko gazawar gwamnati na samar da guraben zubar da shara a unguwanni da kasuwa ko asibitoci.
Ambaliya ruwa na da matukar illa ga jama’a domin takan zama sanadin rasa rayuka da dukiyoyi da tsirrai da dabbobi da wasu abubuwa masu muhimmanci ga rayuwa dan’adam. Duk sassan kasar nan na fama da wannan annoba ta ambaliya ruwa sakamakon rashin tsari a bangaren jama’a da gwamnatocin kasar nan. Wanda hakan na nuna gazawa daga wajen hukumomin kula da muhalli wajen hora duk wanda aka kama da laifin gurbata muhalli.
Ya zama dole hukumomin kula da muhalli su hada kai da ‘yan jarida wajen wayar da kan al’umma domin kare su daga illolin da ke tattare da gurbataccen muhalli.
Nijeriya na fama da matsaloli daban-daban sakamakon karuwar jama’a , ci gaban da zamani ya kawo sakamakon samuwar masanaantu wannan ya sa an samu matsaloli da yawa kamar su, kwararowar Hamada da zaizayar kasa, Karuwar yawan jama’a da sare gandun daji na taimaka wa wajen lalata muhalli,
Muhalli ya kunshi ruwa da kasa da iska da duk wani abu da ke sama da kasa wanda za mu iya gani da kuma wanda ba za mu iya gani ba. Wannan dangantaka da ke tsakanin mutum da muhallinsa ta samo asali ne ta yadda Allah ya halicci duniya, a matsayin cudanni in cude ka tsakanin muhalli da dan’adam da tsirai da ruwa da kasa.
Hakan na nuna cewa, kowane bangare ba zai iya rayuwa shi kadai ba, ita wannan cudanya ita ke nuna yadda muka jefa muhalli cikin rudani kamar yadda muka sani sakamakon harkokin dan’adam na yau da gobe, suka jefa muhalli cikin rudani domin yawan amfani da abubuwan da ya samu a duniya yakan juya su ta yadda yake so domin biyan bukatarsa.
Wasu daga cikin illolin da rayuwar dan’adam na son zuciya ta samarwa a muhallinmu sun kunshi wasu daga cikin abubuwan da aka gabatar a farkon wannan magana.
Kwararar jama’a zuwa birane sakamakon neman tsira ko samun abin sa wa a bakin salati ya jawo gurbacewar muhalli da rashin shirin gwamnatocin a kan yawan baki da ke shiga birane ba tare da ka’ida ba. wannan yana jawo barazana ga rayuwar mazauna birni, yakamata gwamnatocin jihohi su samar da kayayyakin more rayuwa a kauyuka domin rage kwararar baki zuwa birane.
Wannan matsala ce da ke damun kowane bangare na Nijeriya, domin hanya ce da kasar noma ke zaizaye wa ta hanyar gudun ruwan sama, ko iska mai karfi da ke kwashe saman kasar noma ta mai da ita maras amfani, ko an yi shuka ba za a sami wani abin kirki ba, sakamakon kwashe sinadarai da ke zama kamar taki ko kuma abincin da tsirai za su ci domin su girma.
•Illolin Da Ke Tattare Da Gurbata Muhalli Ga Rayuwar Dan’adam
Rahotanni daga Hukumar kula da lafiya ta duniya (WHO) sun nuna cewa, a kalla gurbata muhalli na sanadiyyar salwantar rayukan kusan mutum miliyan goma a duniya a kowace shekara.
Wani babban abin tashin hankalin shi ne Nijeriya na daga cikin kasashen Afirkan da wannan matsala ta yi kamari a cikinta, kuma ita ce ta hudu a cikin jerin kasashen duniya da ake fama da wannan matsala ta gurbata muhalli. Domin kuwa kididdiga ta nuna cewa, duk cikin ‘yan Nijeriya dubu dari, akwai mutum dari da hamsin da ke mutuwa sakamakon shakar gurbatacciyar iska a kwace shekara.
A kasar Afganistan mutum 406, a Pakistan 207, a Indiya 195 ke mutuwa daga cikin mutum 100,000 a kowace shekara, in aka kwatanta da Nijeriya sai a ga abin ba kyau. Hattana kasashen da suke da manyan masana’antu za ka ga akwai dama-dama, kasashe irin su Chana wadda mutum 117 ke mutuwa daga cikin mutum 100,000; Rasha mutum 62; Jamane mutum 22; Tarayyar Turai 21; Amurka, 21; Jafan, 13, sai kuma Kanada mai mutum 12.
Kamar yadda wani rahoton shekara da ya fito daga “Health Effectibe Institute” wanda mujallar “Global Air Report” ta wallafa ya nuna cewa, Nijeriya da wasu kasashe 10 na daga cikin muhallin da za a iya shakar gurba tacciyar iskar da za a mutu, sakamakon amfani janaratoci da hayakin da ababen hawa ke fitarwa da kona daji da kona shara da makamantansu. Sannan kuma daga cikin abubuwan da ke gurbata iskar akwai yoyon iskar Gas kamar abin da ke faruwa a jihar Ribas da wasu makwabtanta.
A rahoton WHO na shekara ta 2016 ya nuna cewa, Anaca da Kaduna da Aba da Umuahiya na daga cikin manyan birane 20 a Afirka da suka fi fama da gurbacewar iska.
Haka kuma rahoton ya ci gaba da cewa, kusan birane 3,000 da ke fadin duniya, akalla wadanda ke da yawan jama’ar da suka kai mutum miliyan 100,000 ke fama da matsalar gurbacewar iska. Bugu da kari kuma an bayyana cewa, garin birnin Kaduna da Aba da Umaahiya da ke da matsayin na 8 da 9 da kuma 19 daga cikin birane 20 na fama da gurbacewar iska.
Masana sun nuna cewa akwai nau’I iri biyu na gurbacewar iska- gurbacewa ta hanyar iskar Gas da kuma hayaki. Kowane nau’I daga cikinsu babbar illa ne, musamman ga rayuwar kananan yara. Bincike ya nuna cewa kashi 93 daga cikin kasha 100 na yara ‘yan kasa da shekara 15 na shakar gurbatacciyar iska. Haka kuma yaro daya na mutuwa daga cikin yara 4 sakamakon shakar gurbatacciyar iska. Gurbatacciyar iskar ta fi yi wa yaran illa ne saboda suna daurin shakar iska a-kai-a-kai. Bayan kisan yara kanana da gurbatacciyar iskar ke yi tana kuma haifar musu da cututtuka iri daban-daban.
Ga manya kuma, shakar gurbatacciyar iska ita ke haifar da mututar kashi 1 daga cikin kashi 4 na jama’a sakamakon ciwon zuciya, kashi 25 daga cikin 100 sakamakon shanyewar jiki, kashi 43 daga cikin 100 miyagun cututtuka sannan sai kashi 25 daga cutar kansa.
Ida ana shan taba kuma babu abinci mai kyau suka kuma hadu da hawan jini, abu na hudu da zai taimaka wajen kashe mutum it ace gurbatacciyar isaka.
An lura cewa wannan annoba ta gurbacewar iska ta fi yawaita a kasashe masu karanci da matsakaicin tattalin arziki, kamar kasar Asiya da nahiyar Afirka da kuma kasashen da ke yankin Gabashin tekun Meditireniyan irin su; kasar Turai da Amurka.
Ganin hatsarin da ke tattare da shakar gurbatacciyar iskar tuni kasashen da suka ci gaba suka mike tsaye wajen kawo karshenta kuma sun samu nasara a kan yin hakan, saboda haka yanzu ba sa fuskantar irin wannan barazana ta shakar gurbatacciyar iska.
Shawarwarin da muke bayarwa da kuma fatanmu a nan shi ne masu ruwa da tsaki da ked a alhakin kula dakile hanyoyin gurbacewar iska su fahimci irin mummunar illar da take da ita a cikin al’umma, Sannan kuma su sani cewa, ya zama wajibi su tashi tsaye wajen kawo karshen gurbacewar iska a kasar nan. Haka kuma muna kira da babbar murya ga gwamnati ta samar da hanyoyin da za a kawar da gurbata iska, sannan a hukunta duk wanda ya yi kunnen kasahi ya karya dokar don ya zama darasi ga na baya.