Connect with us

KIWON LAFIYA

Amfanin Ruwa A Jikin Mutum

Published

on

‘Yan uwa Assalam alaikum. Barkan mu da wannan lokaci, barka mu da sake saduwa a wannan shafi da ke zakulo bayanai domin ku fa’idan tu, ku san yadda jikkunan ku ke aiki.

Ruwa abokin aiki inji malam Bahaushe. Jiki yana bukatar ruwa domin gabatar da al’amuran rayuwa na yau da kullum. Wani zai yi tunanin maganin kishi kawai yake yi; inaa, ruwa ya wuce nan a fagen amfanar da jikin dan Adam. Ina so nayi bayanin amfanin ruwa ta hanoyi guda biyu. Hanyar farko ita ce bayani akan amfanin ruwan da muke sha, ko kuma rawar da ruwan da muke sha ke takawa a jikin mutum. Hanya ta biyu zan bayani akan ruwan jiki, da yadda yake da muhimmanci wajen tallafar kwayoyin halittar jiki.

 

Ruwa Ya Na Manyan Aiki Guda Hudu

Ruwa na da muhimmanci a jikin mu ta manyan fuskoki guda uku. Na farko yana samar da muhallin narkewar sindarai kala kala a jiki (water as a solbent). Na biyu yana aiki a matsayin mai bada kariya daga sidewar guraren da ake samu yawan motsi a jikin mutum. Ita gugar dake jawo sidewar ana kiranta (friction) a turance. A sanadiyyar haka, ruwa ya zamto mai bada kariya ga gabban jiki. Sannan na hudu: yana taimakawa wajen daidaita yanayin dumamar jiki (water regulates body temperature).

Akwai ruwan dake cikin kwayoyin halittu, akwai kuma wanda yake a wajen su, yake kewaye dasu, ko kuma suke wanka a ciki. Bari mu fara da ruwan dake a wajen kwayoyin halittu da muhimmiyar rawar da yake takawa ta tallafar rayuwa. Misalan su,  su ne: ruwan hawaye, ruwan gumi, ruwan jini, ruwan majina, ruwan maniyyi, ruwan dake zagaya kwakwalwa, ruwan jakar zuciya, ruwan jakar huhu, ruwan kogon kayan ciki, da irin su.

Ruwan kogon dake dauke da kayan ciki. Ma’anar kogon ciki shi ne inda ake samun su hanta, koda, tumbi, hanji, saifa, madaciya, kitse da sauran su. Anan, ana kiran wannan ruwa “peritoneal fluid”. Yana taimakawa kwarai wajen rage karfin gogar juna da ke faruwa tsakanin kayan ciki, saboda idan zaku dubi kayan ciki, sun kasance a waje kuntatacce wanda sashen su zai zamo mai cudanya da sashi. Bugu da kari, wannan ruwa na tallafar kayan ciki.

Huhu ma da yake cikin kogon kirji yana rufe ne a cikin rigarsa da ake kira “pleura”. Wannan riga ta rabu gida biyu: akwai wadda take damfare da jikin huhun, wadda it ace ta lankwasa ta rufe kasuwan hakarkari daga ciki. Lankwasawar da tayi ya samar da rubi guda biyu, riga ta ciki da kuma riga ta waje. A tsakanin su ne aka samun wannan ruwa da yake kare gugar da huhu ke yi wa kogon kirji daga ciki, lokacin da muke numfashi.

Akwai kuma wani ruwan na musamman da kwakwalwar mu ke yawo a ciki, ana kiransa “cerebrospinal fluid”. Wannan ruwa kewaye yake da kwakwalwa da laakar mu, kuma yana zagayawa a kullum sau biyar daga mabubbugar sa izuwa karshe, sannan izuwa mabubbugar sa dai. Kenan idan mutum ba musulmi bane, aikin banza yake yi, tun da kwakwalwar sa tana alwala sau biyar kowacce rana! Wannan ruwa shi yake hana mu jin nauyin kwakwalwar mu a cikin kan mu, saboda yawo take yi a cikin sa. Yana dauke da sinadaran da kwayoyin halittar kwakwalwa ke amfani dasu wajen gudanar da ayyukan yau da kullum. A duk irin wadannan misalai, ruwa yana hana sidewar gabbai, sannan yana bada kariya.

A ci gaba da aikin ruwa wajen  maganin sidewar guraren da ake samun yawan motsi a jiki, ga wani misalin. A mahadar kashi da kashi (gwiwar hannu, gwiwar kafa), akwai wani ruwa mai yauki-yauki da ya zagaye dukkan mahadar. Ana kiran sa “synobial fluid”. Ana samu makamancin wannan ruwa a jakar zuciya, saboda ya hana ko ya rage karfin gugar da zuciya ke yiwa makwabtan ta yayin da take bugawa ko harba jini zuwa sassan jiki. Anan, ana kiran wannan ruwa “pericardial fluid”.

Yau da gobe taki wasa. Jiki na da naka kullum na rasa ruwa mai yawa a sanadiyyar ayyukan da mafi yawa su na faruwa ne domin a tsaftace Jiki, kamar yadda bayani ya nuna a rubutun da ya gabata. Hanyoyin da ruwa ke barin jikin mu sun hadar da gumi ta sanadiyyar wani aiki ko motsa jiki, ko shiga wani yanayi mai tsanani, ko numfashi ( saboda iskar da ke fitowa daga huhu dauke take da danshin ruwa.), ko bawali, ko bayan gari. Babbar hanyar da muke rasa ruwa a jikin mu ita ce sanadiyyar fitsari.

Abin da zai baku mamaki shi ne: kullum jikin mu na rasa lita 2 da digo 5 ta ruwa ta hanyoyin ( fitsari gumi, numfashi, magana, da bayan gari), sannan kuma yana maye gurbin lita 2 da digo biyar din ta hanyar cin abinci, shan ruwa, da ayyukan cikin gida na kwayoyin halitar jiki. Kenan wajibi ne akan kowa ya kula da shan ruwa ko dan saboda ya kaucewa matsalar rashin daidato a jiki; ma’ana ruwan da aka rasa, yafi wanda aka samu yawa.

Ta yaya muke rasa ruwa ta hanyar magana?  saboda yayin da muke magana,  iskar dake fitowa daga bakunan mu tana dauke da danshin ruwa. Akwai kuma danshin ruwan da ke fita tare da bayan gari. Muna rasa ruwan dake cikin miyau, da ruwan dake sauran kuttun sinadarai wato “glands” ke zubowa, da sauran su. Idan aka tattare duk wannan ruwan da muke rasawa kullum, ana rasa kimanin lita 2 da rabi na ruwa, kwatankwacin yawan gwangwanin maltina guda goma (10). Wannan shi yake nuna  bukatar mu dinga sha ruwa domin maye gurbin abin da aka rasa.

Bari na fara da abubuwwa na zahiri da muka fi sani kuma muka fi sabawa dasu: shan ruwa yana maganin kishi. Kishirwa alama ce dake nuna cewa ruwan jiki yayi kasa. Na biyu: ruwan da muke sha kullum na da amfani wajen taimaka mana maye gurbin ruwan da aka rasa ta wadancan hanyoyi. Sannan yana taimaka wa wajen markade da narka abincin da muka ci, da fito da sinadaran amfani dake cikin wannan abinci da zasu amfane mu.  Gwargwadon aikin da kake yi, gwargwadon yawwan ruwan da ya kamata ka/ki sha.

Yanzu bari muyi duba izuwa ruwan dake cikin kayoyin halitta. Kamar yadda bayani ya gabata a rubutukan da suka wuce, akwai kwayoyin halitta kala kala a jikin mutum. Wasu suna dauke da ruwa mai yawa, wasu madaidaici, wasu kuma kadan. Misali: kwan da mace take yi duk wata, wanda idan bai hadu da ‘ya’yan rai na maniyyi ba zai zama bakon ta na wata yana dauke da ruwa mai yawa. Kusan shine kwayar halitta mafi girma kaf jiki. Shi kuma dan maniyyi guda daya shi ne mafi kankantar cikin su, saboda haka yana da ruwa mara yawa.

Kwayoyin halittar tsokar nama, nada matsakaicin ruwan rayuwa a cikin su. Amma kam kwayoyin halittar kashi da na fata nada ruwa dan kadan. Shi yasa kashi yake a sandare. Duk da haka, ruwan dake cikin wadannan kwayoyin halittu yana taimaka musu wajen samar da koramar da ‘gabban’ dake ciki zasu yi wanka, su samu abinci, har ma suyi musayar sakonni a tsakanin su. Saboda muhimmancin wannan ruwa a jiki yasa ake kiran sa da ‘ruwan rayuwa’. Ruwan rayuwa shi ne gabban dake cikin kwayar halitta tare da ruwan da suke wanka a ciki; a turance kuma “protoplasm”.

Sinadarai kala kala suna lunkaya a cikin ruwan jiki, wato ruwan dake ciki da kuma kewaye da kwayoyin halittu.Misalin su shi ne (glucose, amino acids, proteins, sodium, bicarbonate, calcium, potassium sauran su). Wasu sun fi yawa a cikin, wasu kuma a wajen. Anan, ruwa na a matsayin wani dandali inda wadancan Sinadarai ke kai kawo tsakanin ciki da wajen kwayar halitta. Kowanne daga cikin su akwai ma’aunin yawan sa a waje, da kuma ma’aunin yawan sa a cikin kwayar halitta. A duk sanda aka sami sabani; Misali wanda yafi yawa a ciki ya fito ya taru a waje, jikin ka/ki zai ta kokari har sai an mayar da wancan sinadari ainihin bigiren sa.

Ruwa yana daidaita dumamar jikin mutum. An auna dumamar jikin mutum lafiyayye, inda aka samu daraja 37 a ma’aunin Celsius. Yanayin dumamar ruwa (zafin sa ko sanyin sa) baya sauyawa da wuri; ko kuma nan take. Misali: tafasasshen ruwa ba zai huce ba, sai ya dauki lokaci, kamar yadda daskararriyar kankara ba zata narke ba sai ta dauki lokaci. Idan ana bukatar sauyin da sauri, sai dai a sa tafasasshen ruwan a furji ko kuma a saka kankarar a tukunyar dake kan wuta.

Wannan dabi’a ta ruwa, ta rashin sauya yanayin dumamar sa da wuri ta sanya ruwan dake jiki jumurin dakile yawan sauyawar dumamar jikin mu. An saita ma’aunin a daraja 37. Amma wannan baya nuna cewa dumamar jiki zata yi ta zama a 37, saboda ana samun sauyin a ciki da wajen jiki nwanda ka iya yi wa wannan saiti karan tsaye.

Kasancewar kwayoyin halitta tsullum suke cikin ruwan jiki, kuma yanayin dumamar ruwa bata sauyawa da wuri yasa zafin jikin mai lafiya ya tsaya a ma’aunin Celcius da daraja 37. Kenan zamu iya cewa ruwan yana sanyaya jiki. Duk lokacin da wani abu yasa dumamar jiki yayi sama da 37, wannan shi ake kira “Zazzabi”. Alamu ne dake nuna cewa wani bakon abu, irin su kwayar cuta, sun shiga jiki.

 

Mu hadu a wani makon da yardar Mai duka
Advertisement

labarai