Sakamakon wani binciken da kwararrun malaman kula da lafiya suka yi ya nuna cewar irin muhimmancin da yake tattare da yawan shan ruwan dumi, ko kuma ruwa wanda ba mai sanyi ba a maimakon sha da amfani da ruwan sanyi a ko wanne lokaci.
A duk lokacin da yanayi ya canja wato aka shiga yanayi na zafi, zaka ga duk wani abu mai sanyi yana kasuwa matuka.
Babban dalili kuwa shine aka gani kawai mafita ga matsanancin kishi da mutum kan ji da kuma rage radadin zafi.
Likitoci masu yawa da suka yi hira da kafar labaran mu sun bayyana cewar ruwan dumi kan warkar da marasa lafiya musamman cututtukan da suka shafi ciki.
An gano cewar maimakon samun sauki akan fada nema cikin matsaloli ne na kiwon lafiya.
Shan ruwan dumi ko kuma ruwan da bashi da sanyi sosai na da amfani kamar haka:
1. Yin wanka da ruwan dumi na kare mutum daga kamuwa da ciwon sanyin kashi.
2. Yana kare mutum daga kamuwa da cutar hakarkari wato ‘pneumonia’
3. Za a iya samun kariya daga kamuwa daga mura.
4. Yana kuma kawar da ciwon ciki.
5. Yana kara karfin jiki musamman a lokacin zafi da aka fi yawan jin gajiya.
6. Yana taimakawa wajen zurfin tunani.