Nazarin Niki Wilson:
Niki Wilson ta bayyana cewar a lokacin da ta fara balaga, sai ta fara daina yin wasa da maza a makaranta, mahaifiyarta ta tatauna da ita a kan al’amarun da suka shafi jima’i, inda ta bata wasu shawarwari da kuma gargadi kan yadda zata kare kanta daga wata illa ko abin takaici a sanadiyyar jima’i.
Wannan ba shakka shawara ce mai kyau, domin hatta hukumar lafiya ta duniya ta ce, a fadin duniya sama da mutane miliyan daya a duk rana suna kamuwa da kwayoyin cuta na jima’i (STD).
Wasu daga cikin wadannan kwayoyin cuta na iya hana haihuwa, wasu ma na iya haddasa cutar da ta fi haka din. Akwai dalilai masu yawa da za su sa mu hana wadannan miyagun baki samun wuri a jikinmu.
Miyagu daga cikin irin wadannan kwayoyin cuta na jima’i watakila su suke sa ba a mayar da hankali a san cewa akwai wasu daga cikin kwayoyin da ke kai- komo a ruwan jima’in masu saduwa, na iya kasancewa masu amfani.
To ya kuma idan aka ce a kokarin da ake na kare kanmu daga nau’in wadannan kwayoyin masu cuta da muka sani, muna asarar masu amfani da daga cikin kwayoyin?
Bincike da yawa da aka yi yana nuna cewa ya kamata a sake nazari tare da yi was hi al’amarin kallon tsanaki.
Ba wani sabon labari ba ne cewa kananan kwayoyin halittu, kamar su bakteriya da bairus (bacteria, birus), suna da matukar amfani ga lafiyarmu. A cikin jikin kowannen mu akwai kwayoyin masu cutarwa da kuma masu amfani. Idan aka samu bambanci kan yadda yawan kowanne ya kamat ya kasance a jikin mutum, to sai a samu matsala.
Misali, akwai kwayar (yeast, candida) da ake samu a farjin mace, wadda wata kwayar halitta ta bakteriya (lactobacillus) take yaki da ita. To idan ya kasance wani abu ya hana wannan kwayar bakteriya aikinta, sai ita waccan halittar ta farko ta mamaye farjin, abin da zai sa mace ta kamu da wata cuta da ke sa kaikayi a farji (yeast).
Jikinmu ya samo asali da rayuwa tare da kananan halittu (microbes). Wadannan ‘yan mitsi-mitsin kwayoyin halittu (bacteria, fungi, birus) suna jikin fatarmu da hanjin mu da kuma farjin mu.
Duk da cewa ba wani abu ne da za aso ayi tunani ba, yadda wadannan ‘yan halittu ke karakaina a cikin hanjinmu ba, amma kuma a kullum muna kara fahimtar cewa wadannan halittu suna taka muhimmiyar rawa a halittar shi kansa jikinmu.
Mataki na farko na fahimtar rawar da su wadannan ‘yan halittu suke takawa shi ne a gane su. Duk kuwa da cewar ba mu san da yawa daga cikinsu ba zuwa yanzu, akwai misalai masu ban sha’awa da za su karfafa mana guiwa mu mayar da hankali a kansu, in ji Chad Smith masanin kimiyya a jami’ar Tedas a Amurka.
Mu dauki misalin wani kwaro (pea aphids) da ke tsotse ruwan jikin kayayyakin amfanin gona masu ba wa jikin mutum abubuwan gina jiki (legumes), kamar wake da gyada da dai sauran makamantansu.
To yadda kwarin ke cin moriyar rayuwarsu na da alaka da kwayoyi (na cuta) masu amfani da ke shiga jikinsu a lokacin jima’i. Tasirin hakan kuma ya hada da bijire wa kwayoyin cutar da suke kashewa ko hana wanda yake dauke da su haihuwa da jure wa zafin rana sannan kuma da iya rayuwa a kan tsirran da ba wadanda suka saba cin amfaninsu ba, har sai sun samu abinci.
Wannan bai kare ba, domin akwai wasu nau’ukan sauro da suke yada wata kwayar bakteriya a tsakaninsu a lokacin jima’i, kuma wannan kwayar tana mamaye hanjinsu da kwalatansu da kuma jikin kwayayensu.
Ana ganin wannan lillibi na wanna kwaya ta halitta ta bakteriya tana ba dan tayin wannan kwai abinci, abin da ke sa dan tayin (ko tsutsar) ya yi saurin girma kwana biyu zuwa hudu fiye da kwayayen da ba su samu wannan sinadari ba.
A karshe kuma kwayoyin cutar jima’i masu amfani, an gano suna karawa halittar fungi juriyar zafin rana, tare da taimaka wa duk fungi din da take da kwayoyin saurin girma.
To amma kuma ya lamarin yake a mutane? Yanzu dai mun san cewa akwai wani misali da zai sa mu yarda cewa kwayoyin halitun (cutuka) da ke yaduwa a lokacin jima’i na iya amfanar wasunmu.
Wannan kwayar halitta ta bairus ce (GB birus C) kuma an fi saninta da hepatitis G birus (HGB). Kwaya (r cuta) halitta ce da ake yada ta a lokacin jima’i, wadda a karan kanta, babu alamar tana haddasa wata babbar cuta, ko da yake yawanci ana ganinta da wasu kwayoyin cuta na bairus kamar HIB.
Wannan kwayar cuta (GB birus C) za ta iya rage hadarin uwa ta yada wa jariri kwayar cutar kanjamau, wato HIB.
Wani nazari da aka yi na wasu bincike guda shida ya gano cewa kwayar bairus din (GB birus C) tana da alaka da rage kashi 50 cikin dari na rage mutuwar masu dauke da kwayar cutar kanjamau.
Masana kimiyya na ganin kwayar tana yin haka ne ta hanyar rage karfin kwayar HIB na raunana kwayoyin halittar (cells) garkuwar jikinmu. Ana ganin za kuma ta iya kara zaburar da sauran sassan garkuwar jikinmu su yaki kwayoyin cutar ta HIB sosai.
Hakanan kuma dai ita wanna kwaya mai amfani (GBB-C na iya yaduwa daga uwa zuwa jariri. Wanna kuma ba karamin alheri ba ne domin za ta iya rage hadarin uwa ta yada wa jaririnta kwayoyin cutar mai karya garkuwar jiki.
Bada dadewa bane kuma ana ganin kamar ita kwayar GBB-C din tana rage hadarin mutuwar wadanda kwayar cutar Ebola ta kama, inda take rage tasirin kwayar cutar a jikin mutum.
Gano irin wannan amfani na ban mamaki na kwayoyin da ake yadawa a lokacin jima’i, zai sa mu yi mamakin irin asarar da muke yi, in ji Betsy Fodman ta jami’ar Michigan a Amurka.
Ta ce a da mun dauka cewa duk wata kwaya da ake yadawa a lokacin jima’i ta cuta ce kawai. Matakan da muke dauka na kariya daga garesu kila sun sa yanzu ba mu da wasu daga cikin irin masu amfanin a jikinmu.
Mai binciken ta bayyana cewa watakila ma akwai wasu kwayoyin halittar (microbes) wadanda ke yakar wasu cutukan, mu ba mu sani ba. Idan kuwa haka ne, akwai su to ka ga hakan zai sa mu rage yawan dogaron da muke yi a kan magunguna (antibiotics).
Ta kara da cewa, ”ba shakka wajibi ne a wani lokaci a yi amfani da magunguna domin cetar rayuka, amma zai fi dacewa ka samu wani abin wanda ya fi dacewa, wanda kuma zai je kan kwayoyin cutar ne ya yake su kai tsaye ba tare da yin dan wani abu daban ba (illa).
Ba mu da tabbas kan wacce kwayar halitta ce da ake yadawa a lokacin jima’i take da amfani, amma dai Fodman tana ganin Lactobacillus, wato bakteriyar da ake samu a madarar yogot (yoghurt), wadda kuma daman akwai ta a jikin dan Adam, tana daya daga cikinsu. Ta ce watakila ma akwai wasu masu amfanin wadanda ba a kai ga gano su ba.
Wannan duka kamar wani labari ne mai dadin ji? Zai iya kasancewa akwai wasu tarin kwayoyin da ake yadawa lokacin jima’i masu amfani ga lafiyarmu, wadanda ba musan su ba sosai.