Amfanin Yi Wa Mace Gyarar Maida- Tsohuwa-Yarinya – Shakirat Isiyaku

Mace sai da ado, kwalliya mizanin mata, kwalliya mai tsone idon kishiya, kwalliya kasaitar mata, wannan kirari kadan ne daga cikin rumbun taken da ake yi wa kwalliyar mata. Mata tun fil-azal an san su da kwalliya, kuma tana daya daga cikin abin da ke kara musu kima da martaba a idanun mazajensu.

Saboda muhimmanci kwalliya ga mata, a wannan makon Shafin Adon Gari ya yi tattaki na musamman zuwa wurin wata gwanar iya kwalliya da gyaran jikin mata domin fayyace wa masu karatu yadda sha’anin kwalliya yake musamman a wannan zamanin mai cike da ci gaban ado kala-kala.

 Gwanar kwalliyar ta yi bayanai takaitattu kuma masu alfanun gaske kan bunkasar kwalliya da gyaran jiki a wannan zamanin har ta kai ga ko da mace ta tsufa, akwai gyarar da za a yi mata ta koma tamkar yarinya. Bugu-da-kari, akwai kwalliyar da ake kara wa mata dogon karan hanci ya fito sak! Sannan ta hutar da maza ko mata da za su iya tsunduma cikin duniyar tunani kan mene ne tasiri da amfanin kwalliyar da gyaran jiki, kasancewar ta warware zare da abawa kan hakan. A karanta yadda hirar ta kasance kamar haka:

Ko za mu iya sanin sunanki?

Sunana, Hajiya Shakirat Isiaku.

Muna so ki fada mana tarihin rayuwarki a takaice?

An haife ni a Jihar Zamfara, Gusau. Na yi makarantar, Sakanadare ta Sambo da ke nan Gusau. Na gama karatuna ne a makarantar koyon kimiyya da fasaha watau, “Federal Polytecnic Kauran Namoda, Gusau. Na karanta “Business Administration.” Ni Matar aure ce, ina tare da Mijina Alhaji Isiaku.  Ina kuma zaune ne a Unguwar Dosa Kaduna.

Ana ta kiraye-kirayen mata da su sha damarar neman na kai domin tallafa wa iyalansu, ko kina da wani abu da ki ke yi ta fannin kasuwanci ko aikin gwamnati?

Ina sana’ a ne. Ina da ‘Saloon’  wajen gyarawa Mata gashi,  kuma wajen gyaran jiki wa Mata. Wanda ake cewa, Alawa, da sauransu. Ina yi wa Mata gyaran fuska, wanda ake kira ‘make-up.’  Za mu iya batar wa Mace da bille, idan ma tana da billen kuma ba ta bukatarsa.

Ko za ki fada mana da me-da me, ki ke yi da kuma amfanin su a jikin mata?

Gaskiya mahinmacin wannan kwalliyan kuwa shi ne, yana karawa Mata kyau, da laushin jiki. Sai jikin Mace, ya yi laushi kamar tamkar jikin jariri. Kuma shi gyaran fuska wanda ake ce ma, ‘make-up’ yana kara wa Mata kyau, kuma yana kara wa Mata dogon hanci, shi ake kira “nose contouring”.

A takaice za a iya cewa, kina iya mayar da tsohuwa yarinya da wannan sana’ar kenan?

Gaskiya, za mu iya canza tsohuwa ta dawo yarinya. Idan ma tana da bille wanda ake cewa ‘tribal mark.’  Za mu  iya boye shi, ba za a gane tana da shi ba. Kuma ina hada man shafawa,  da sabulu da man fuska, wanda idan Mace tana da kuraje ko  ‘Pimples’ za ta warke kafin sati daya, in sha Allah.  Man shafawana ba na kemikal ba ne.  Na gargajiya ne, wanda ake ce ma ‘Organics.’

Hajiya Shakirat, ya ya tsarin makarantarki ta koyar da gyaran jiki da kwaliyya take?

Gaskiya Muna koyar da  Mata da dama. Akwai tsarin koyarwa na sati biyu, sannan akwai na wata daya.  Duk wanda mutum yake so.

Idan Za mu koma bangaren iyali, ki na da yara 6, kuma ga ki ‘Yar kwalisa, kamar yarinya karama. Ta ya ya ki ke kula da kanki da iyali, da kuma gudanar da harkar makarantarki da kamfaninki?

Gaskiya ne, ina da yara 6, amma ina godiya ga Allah Madaikakin Sarki.  Kamar yadda ku ka sani ne cewa, ‘its neber easy’ yadda zan kula da yarana da mijina da kaina.  Amma cikin ikon Allah, komai yana zuwa mani da sauki.

Idan na tashi karfe 4 na asuba,  sai na sa masu ruwa a wuta,  idan ya yi zafi, sai na dibi nawa a cikin ruwan dimin na yi wanka, sai na yi Sallah. Ina idar da Sallah, sai na tashi yaran su je su yi Sallah su yi wanka, su shirya zuwa makaranta.

Ni kuma sai na ci gaba masu da girkin da za su ta fi da shi makaranta.  Su na wucewa makaranta, sai na zuba wa Maigida na shi abincin a ‘kula.’ Ni ma sai na fara shirin zuwa shago. Amma Mu na bude shago karfe 9:30 na safe ne, kuma mu  rufe shago karfe 6; 30 na yamma.  Sai in kuma komawa gida in fara girke-girken yamma.

Baya ga Kaduna, ko kina zuwa gari-gari kan wannan sana’a ta wankan Amare, ko a iyaka Kaduna kawai ki ka tsaya?

A’a, ba Kaduna kawai ba. Mu na zuwa garuruwa yin gyaran jiki da gyarar fuska wanda aka fi sani da ‘make-up’.

 

Kamar misalin tsawon kwana nawa gyara da wankan Amare ke daukar ki, kafin ki kammala?

Akwai wasu Amare da za su ce kawai gyaran jiki na kwana uku suke so.  Akwai wanda za su ce, na sati daya suke so.

Ko za ki iya fada mana yadda ki ka koyi wannan sana’ar, kuma a ina ki ka koya?

Gaskiya ba a nan na koyi gyaran jiki da Man shafawa ba, a Kasar Indiya na koya. Wata ‘Yar Pakistan ta koya mani, a na ce mata Ummah Dinah.

 

 

Exit mobile version