Zubairu M Lawal" />

Amina Muhammad Ga Mata: Ku Zama Jakadun Zaman Lafiya A Duniya

Hajiya Amina J. Muhammad, Mataimakiyar Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, ta bayyana haka . Da take jawabi a wajen taron tabbatar da ayyukan Majalisar Dinkin Duniya mai taken mahufofin cigaba mai inganci ga rayuwan marasa galihu karo na 75 , wanda ya gudana a harabar cibiyar yada labarai na Majalisar Dinkin Duniya dake birnin tarayyar Nijeriya  Abuja.

Mataimakiyan Sakataren ta ce; matsalolin dake faruwa a Duniya yanzu na rashin samar da dauwamamen zaman lafiya, mata su na da rawar da za su taka domin samun zaman lafiya mai inganci ko’ina.

Ta ce; duk abinda naminji zai yi yana karkashin mace ce, haka zalika duk abinda yara zasuyi suna samun tarbiyya ne tun daga gida.

Yara su na samun tarbiyan abubuwa masu kyau daga gida a gaban iyaye kuma suna samu marasa kyau a gaban iyaye. Saboda yaro yana tashi a gaban iyayansa da abinda ya koya.

Hakki ne a kan iyaye su rika sanya ido a kan ’ya’yansu. Mace ita ce da gida ita ke kula da tarbiyyar yaran a gida. Dole uwa ta rika sanya ido a kan yaran ta ta lura da halayensu. Waye ya ke yin mai kyau? Waye ya ke yin maras kyau?

Tun ice ya na danye a ke tankwasa shi; yaro ya na karami ake koyar dashi abubuwa masu kyau idan yayi mara kyau a hane shi.

Amma sakaci yanzu iyaye basu damuwa da tarbiyyar yara su na barin yaro ya aikata abin da ya ke so wasu su kan girma da munanan dabi’u.

Haka zalika mace ita zata rika kulawa da maigidanta ta na ba shi shawara tagari , tana tabbatar da sana’ar da ya keyi .idan yana abu mara kyau idan ta ki masa dole ya chanza ai maza suna samo abubuwan saboda mata ne .

Mace na da dadin baki da zata sasanta tsakanin mazaje da basu jituwa da juna ta haka zata tabbatar da zaman lafiya a tsakanin su.

Yaron da ya tara daruruwan al’umma maza da mata da yara kanana, Hajiya Amina Muhammad, ta yi kira ga yara da su zama masu tausayi da jin Kay da taimakon iyaye , da zuwa makaranta domin samu Ilumi mai amfani.

Exit mobile version