Daga Zubairu M Lawal,
Mataimakkiyar Sakataren majalisar Dinkin Duniya Hajiya Amina Muhammad, ta kaddamar da gangamin cigaban Muradun karni guda 17 wanda zai daura matasa kan ayyukan yi a Duniya.
An kaddamar da wannan gangamin cigaban muradun karnin ne a babban birnin tarayya Abuja. kaddamarwan da ya samu halartan manyan baki daga gurare dabam dabam ciki harda Furaministan karsar Norway an kuma yaba masa game da namijin kokarin da ya yi akan wannan aza hasashin kaddamar na ‘take the ball’.
Muradun karnin na gina kasa mai taken (#TakeTheBall campaign to promote the Sustainable Debelopment Goals) (SDGS).
Tsari ne na mugudu tare mu tsira tare domin cigaban kasashen mu, ta hanyar gina yara da ilumin mai inganci da samar da makarantu masu inganci da samar da ayyukan yi ga matasa..
Da kuma koyar da dabarun hanyoyin taimakon kai da kai da dai dai to a tsakanin al’umma, da taimakon juna. Wannan muradun karnin zai yi tasiri a yan kin yammacin Afirika.
Mista Mohamed Ibn Chambas ya bayyana farin cikin da yadda za a samu cigaba a wannan tsarin na gina rayuwar al’umma. Shima jami’in UNDP a na hiyar Afirika Mista Ahunna Eziakonwa da Mista Chambas daga SDG duk sun halarci taron tare da nuna goyon baya.