Connect with us

WASANNI

Amoju Pinnick Ya Kafa Tarihi A Hukumar Kwallon Kafar Kasar Nan

Published

on

Amaju Pinnick ya zama mutum na farko da ya fara zarcewa a tarihin shugabancin hukumar kwallon kafa ta kasa wato (NFF) bayan ya lashe zabe karo na biyu da aka fafata tsakanin ‘yan takara hudu

Pinnick, mai shekara 44 ya doke abokan hamayyarsa wadanda suka hada da tsohon shugaban hukumar Aminu Maigari da Taiwo Ogunjobi da kuma Chinedu Okoye wanda tsohon alkalin wasa ne.

Wannan na zuwa ne daidai lokacin da wani jigo cikin harkokin kwallon kafa a kasar nan, ya bayyana cewa ya samu umarnin kotu da ke dakatar da wannan zabe da aka gudanar a ranar Alhamis a jihar Katsina.

Pinnick, wanda mataimakin shugaban hukumar kwallon kafa ta Afirka ne, ya samu kuri’u 34 daga 44 da aka kada a zagaye na farko a zaben mai cike da hayaniya da rikice rikice.

Maigari ya samu kuri’u takwas ne yayin da Ogunjobi ya samu biyu, kuma Okoye ya kasa samun ko kuri’a daya acikin kuri’un da aka kada gaba daya.

A cikin wa’adinsa na farko a karagar mulkin hukumar, Pinnick ya yi fama da ikirarin da Chris Giwa ke yi cewar shi ne ya lashe zaben da aka yi a shekara ta 2014 wanda hakan yakawo tsaiko sosai a harkar kwallon kafa a kasar nan

Hukumar ta shafe tsawon lokaci tana fama da rikicin shugabanci, inda a baya-bayan nan ma sai da Hukumar kwallon kafa ta Duniya FIFA ta gargadi Najeriya a kan yiwuwar dakatar da ita matukar hukumomi ba su daina tsoma baki cikin harkokin kwallon kafa ba.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: