Gidado Ibrahim" />

AMOTEKUN: Matakin Gwamnatin Tarayya Na Dakile Bullar Rikici, Ya Dace

Tun bayan cece-kuce da ake ta faman yi dangane da dacewa ko rashin dacewar kirkirar hukumar tsaro ta ‘Amotekun’ wanda jihohin Kudu Maso Yamma suka yi. Na karanta tare da sauraron mabambantan ra’ayoyi dangane da wannan shiri na Amotekun, tare da martanin gwamnatin tarayya kan lamarin, wanda Ministan Shari’ar Nijeriya, Abubakar Malami ya fitar da sanarwar da a ciki ya bayar da umurnin a dakatar da wannan shiri na Amotekun.

A yayin da mafi yawan masu fashin baki ke kallon abin da budaddiyar zuciyar son wanzuwar zaman lafiya da tabbatar tsaron Nijeriya, su kuma wasu sun tubure saboda tsabar son rai kan cewa dole ne a bar shirin Amotekun ya wanzu. Wadannan mutanen makiya Nijeriya sun samu wasu baragurbi cikin ‘yan jarida wadanda da su ne suke amfani wurin rura wutar lamarin.

Sanarwar da Ministan shari’a ya fitar a bayyane take, kuma bayani ne mai gamsarwa ga dukkan mai bukatar gaskiya, inda ya ce: “Samar da wannan kungiyar ta saba da dukkan wani tsarin dokokin tarayya ko jihohi a Nijeriya. Nijeriya ta na da dokoki da tsarinta, wanda kuma dole ne a kiyaye su don wanzuwar kasar.” Wannan dan jawabin ya isa hujja ga me neman gaskiya dangane da rashin dacewar samar da shirin Amotekun. Su masu neman Nijeriya da sharri babu ta yadda za a iya gamsar da su, domin haka za su yi ruro wutar rikicin don son zuciyarsu.

Doka ta 45 a kundin tsarin mulkin Nijeriya ne ya ba rundunar ‘yan sanda da sauran bangarorin tsaro damar tabbatar da tsaron kasar nan. Wannan yana nuna cewa babu wata jiha ko gamayyar jihohi da doka ta aminta su kafa wata kungiya ko samar da wani shiri da sunan samar da tsaro.

Ko da a ce wadannan jihohin Kudu masu yamma suna da burin samar da wani shiri don tabbatar da tsaro, ai kuwa dole ne sai sun nemi shawarar yadda za su yi a ofishin ministan shari’a, Abubakar Malami, wanda shi ne zai nuna musu hanyar da ta dace ba tare da saba doka ba.

Sashe na biyu na Kundin tsarin mulkin Nijeriya na shekarar 1999 ya fayyace cewa: “Tsaro da walwalar mutane ne muhimman abubuwan da gwamnati za ta sa a gaba.” Domin ganin an kiyaye wannan, gwmanatin tarayya ta samar da rundunar ‘yan sanda, rundunar tsaro ta NSCDC domin tabbatar da tsaron cikin gida, a yayin da su kuma rundunar soja ke kare iyakokin Nijeriya. Gwamnatin Tarayya ta jima tana aiki kafada da kafada da gwamnatocin jihohi wurin yin aiki da rundunar ‘yan sanda don tabbatar da tsaro.

Ai kuwa haka kawai a samu wani yankin kasar nan ya balle da zimmar wai zai kirkiri nashi rundunar jami’an tsaron, zai zama abu mai cike da shakku da zargi. Ya kamata a sani a tsarin mulki irin na dimokradiyya wacce Nijeriya ta doru a kai, duk wani abu na saman teburin shugaban kasa ne. Kuma duk wani mai karfin iko na shugaban kasa, ba shi da wani buri da ya wuce kiyaye rayuka da dukiyar al’ummar da yake mulka.

Wannan ne ya sa kowanne shugaban kasa yake da duk wani rahoton sirri dangane da tsaro. Mun gode Allah da ya kasance cewa mutumin da ke rike da lamurran tsaron kasar nan, kwararren masanin tsaro ne, wato Manjo Janar Babagana Mongonu (rtd), wanda mutum ne da ba zai taba bari a haifar da matsalar tsaro ba. Saboda bayanan sirrin da yake da shi a hannunsa ne ya sa Mai ba shugaban kasa shawara kan harkar tsaro, Manjo Janar Babagana Monguno ya ba gwamnatin tarayya shawarar ta dakile shirin Amotekun da wasu jihohi ke yunkurin yi. Wannan matakan da gwamnatin tarayya ta dauka ya nuna cewa abin da gwamnonin jihohin Kudu masu yamma ke yunkurin yi, shiri ne na tada zaune tsaye.

Rashin basira ne ma mutum ya yi tunanin cewa idan aka bari aka kirkiri Amotekun ba zai zamarwa tsarin tsaron Nijeriya kalubale ba. Misali, tun bayan da tsarin mulki na shekarar 1999 ya samar da hukumomin zabe na jihohi ake ta samun korafe-korafe iri-iri. Zabukan kananan hukumomi sun zama mafi hadari da rashin inganci. Kuma duk da haka sai a bari a kirkiri Amotekun, wanda karshe sai ya fi Boko Haram hatsari.

It is foolhardy to think that Amotekun will not, in the end, create security challenges for Nigeria. For instance, since the 1999 Constitution created State Independent Electoral Commissiaon (SIEC), it has been from one complaint to another. Elections into local councils habe grown progressibely worse under this period. Is it Amotekun that will not become another disaster like Boko Haram?

Za mu ga ta yadda za a iya aiwatar da wannan shirin na Amotekun a karni na 21. Sun yi cika bakin yin amfani da gargajiya wurin samar da tsaro. Shin wannan shirin nasu ba zai ci karo da rantsuwar da shugaba Buhari ya yi na tabbatar da kiyaye rayuka da dukiyar ‘yan kasa ba? Dole ne a dakatar da Shirin Amotekun don a kiyaye afkawa yakin basasa.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari na iyaka kokarinsa wurin ganin ya saita kasar nan kan turbar zaman lafiya. Misali, a watannin baya ne shugaban kasan ya kulle iyakokin kasar nan duk a kokarinsa na son tabbatar da tsaro. Wannan matakin da ya dauka, wanda da farko wasu ke kalubalanta, a yanzu an fara ganin amfaninsa.

Shigo da salon dauke hankali irin su shirin Amotekun, ba su ne ke gaban gwamnati ba a yanzu. Ya kamata jihohin Kudu maso yamma su bi a sannu. Kamata ya yi su mayar da hankalinsu wurin yin abubuwan da za su ciyar da yankinsu gaba, ba kokarin yin fito na fito da tsarin mulkin kasa ba.

– Ibrahim shi ne Daraktan Sadarwa da tsare-tsare na Kwamitin Tallafawa Shugaban Kasa

Exit mobile version