Umar A Hunkuyi" />

Amotekun: Yankin Yarabawa Ya Kafe Kai Da Fata

Shiyyar Kudu maso Yammacin Nijeriya a ranar Litinin sun tsallake wani babban shinge a kokarin da su ke yi na kafa kungiyar tsaro ta ‘yan banga ta Amotekun.

Majalisun Jihohi Biyar da suka hada da Jihohin – Oyo, Ondo, Ogun, Osun da Lagos – sun yi wani taron jin ra’ayin jama’a a bisa kudurin da suke da shi na kafa kungiyar ‘yan banga ta Amotekun a yankin na su, wanda hakan ya sanya suka kara motsa wa gaba a bisa neman halascin kudurin nasu.

Majalisar Jihar Ekiti kadai ta rage ya zuwa lokacin hada wannan rahoton, wacce kuma ta rigaya ta gabatar da nata taron na jin ra’ayin jama’a, majalisar ta ce a yanzun haka tana jiran sa albarkan Gwamnan Jihar ne, Kayode Fayemi, domin dokar ta tabbata.

Masu ruwa da tsaki a cikin dukkanin Jihohin guda biyar sun bayar da cikakken goyon bayansu. Dandazon jama’a ne suka taru a wajen jin ra’ayin nasu. An kuma gudanar da taron ne cikin lumana a kuma cikin murya guda ta goyon baya.

Kungiyoyi masu zaman kansu da dama da suka halarci tarukan da suka hada da kungiyar Makiyaya ta, Miyetti Allah, kungiyar Yarbawa zalla ta, Oodua People’s Congress (OPC), kungiyar Kiristoci ta kasa, Christian Association of Nigeria (CAN), da ma wasu kungiyoyin Musulmi da suka halarci taron duk sun nuna goyon bayansu domin kafa kungiyar tsaron ta Amotekun.

Kungiyoyin sun bayyana goyon bayan na su ne a wajen taron jin ra’ayin jama’an wanda aka gudanar a Ibadan, ta Jihar Oyo.

Musamman a bisa yanda makiyaya a karkashin kungiyar Miyetti Allah Cattle Breeders Association (MACBAN), ta fito sarari ta nuna goyon bayanta domin kafa dokar. Dandazon ‘yan majalisar Sarakuna ta Jihar sun barke da sowa da jinjina a lokacin da tsohon shugaban gungiyar ta MACBAN, Alhaji Yakubu Bello, ya fito yana kalubalantar dukkanin masu nuna kiyayya da kafa kungiyar tsaron ta Amotekun a nahiyar ta kudu maso yammacin kasar nan.

Bello ya ce duk masu yada jita-jitar cewa Makiyayan ba su goyon bayan kafa kungiyar ta Amotekun makiyan kasar nan ne, hakanan masu cewa ana son kafa kungiyar ta Amotekun domin kalubalantar al’ummar Fulani ne su ma makiyan Jihar ne.

Shugaban na Miyatti Allah, ya yaba wa gwamnati a kan kafa kungiyar, yana mai cewa duk masu kwatanta kungiyar tsaron da an kafa ta ne domin kalubalantar Fulani sun yi kuskure.

Bello ya bayyana cewa, al’ummar Fulani da kuma masu masaukin na su sun jima suna zaune a matsayin ‘yan’uwan juna, ya kara da cewa, duk masu sukan kafa dokar kafa kungiyar suna son haifar da kiyayya ne a tsakanin al’ummar ta Fulani da kuma masu masaukin na su, yana mai cewa, ba kuma za su sami nasarar yin hakan ba.

Ya kwatanta Makiyaya da masu kaunar zaman lafiya, amma ya yarda da cewa a cikin kowace al’umma akwai na kwarai da kuma na banza.

A karshe, Bello ya gode wa Gwamna Seyi Makinde, a kan tabbatar da dokar da ya yi.

Daga cikin wadanda suka gabatar da jawabai a wajen taron sun hada da; Aragbaji na Iragbiji, Oba Abdul-Rasheed Olabomi; Oloba na O-Ile, Adekunle Oyeyemi, wani babban jami’in hukumar tsaro ta DSS wada yayi ritaya, Mista Akin Adeyi, shugaban kungiyar mafarauta ta, Hunters Group of Nigeria, kngiyar Musulmi ta, Muslim Youth Organisation (NACOMYO) da sauran kungiyoyin tsaro masu zaman kansu.

Duk kuma sun karfafa samar da hadin gwiwa a tsakanin kungiyar tsaron ta Amotekun da sauran hukumomin tsaro na kasa, musamman hukumar ’yan sanda.

Sun kuma yi nuni da cewa, lallai Amotekun ta tsayu kyam a kan dokokin kasa da kuma dokokin nahiyar ta Kudu maso Yammacin kasar.

Amsar da dandazon taron jin ra’ayin jama’ar ya rika amsawa da, Ba gudu, ba ja da baya, a wajen taron jin ra’ayin jama’an da aka gudanar a Majalisar Dokoki ta Jihar Legos.

Exit mobile version