Daga Rabiu Ali Indabawa
Amurka ta ce ba ta da niyyar janye dakarunta da ke faɗa da ayyukan ta’addanci daga jamhuriyar Nijar, duk da harin da aka kai wanda ya yi sanadiyyar mutuwar huɗu daga cikinsu kusa da iyakar ƙasar da Mali a farkon wannan wata.
Babban kwamandan askarawan ƙasar ta Amurka, wanda ke amsa tambayoyi daga ‘yan majalisar dattawan ƙasar kan wannan batu, ya ce lamarin ba zai kasance hujjar janye dakarun da yawansu ya haura 800 da ke jibge a jamhuriyar ta Nijar ba.
A ranar 4 ga wannan wata na Oktoba ne wasu ‘yan bindiga suka kai harin kwanton ɓauna a kan ayarin sojojin Nijar da na Amurka da ke sintiri kusa da iyaka da Mali, inda sojojin Nijar da na Amurka suka rasa rayukansu.