Amurka Ce Babbar Barazana Ga Duniya Ta Fuskar Tsaron Yanar Gizo, In Ji Kakakin Ma’aikatar Wajen Sin

Daga CRI Hausa

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya yi kira ga sassan kasa da kasa, da su yi hadin gwiwar bankado asirin Amurka, tare da kin amincewa da manufofin ta masu barazana ga tsaron yanar gizo, da masu sabawa dokokin kasa da kasa.

Wang wanda ya yi wannan tsokaci, yayin taron manema labarai na Litinin din nan, lokacin da aka yi masa tambaya game da kutsen da Amurka ta yi, cikin rumbun adana bayanan abokan huldar kamfanin Microsoft, ya ce wasu rahotanni ma sun nuna cewa, hukumomin tsaron Amurka na mikawa kamfanin na Microsoft umarnin sirri har sau 2,400 zuwa 3,500 a duk shekara, tsakanin shekaru 5 da suka gabata, da nufin neman tatsar bayanai daga kamfanin.

Don haka a cewar Wang Wenbin, dalilai na zahiri na tabbatar da cewa Amurka ce babbar barazana ga tsaron yanar gizo a duniya.

Da ya tabo batun yadda a kwanakin baya bayan nan, wasu wadanda aka ce masana kimiyya ne suka sanya hannu, kan takardar dake ayyana bukatar sake bude bincike, game da lalubo asalin cutar COVID-19, Wang Wenbin ya ce haka wani yunkuri ne na dora laifi kan wasu, da siyasantar da batun binciken, wanda wasu daidaikun kasashe ke yi, ta fakewa da binciken kimiyya.

Wang Wenbin ya kuma bayyana cewa, Sin na bayyana matukar damuwar ta, da kuma cikakken rashin amincewa da matsayar Australia, game da yadda kasar ta dakatar da Papua New Guinea daga karbar rigakafin COVID-19 da kasar Sin ta samar. Yana mai cewa Australia ta keta hurumin tallafin jin kai.

Game da martanin sa don gane da kalaman Amurka da Birtaniya, kan cewa wai Sin na yunkurin sarrafa alakar hukumomin kasa da kasa kuwa, Wang Wenbin ya ce zarge zargen kasashen biyu, yunkuri ne kawai na bata sunan kasar Sin. (Mai fassarawa: Saminu daga CRI Hausa)

Exit mobile version