Rabiu Ali Indabawa" />

Amurka Da China Sun Cimma Matsaya A Kan Cinikayya Tsakaninsu

Amurka da China sun cimma matsaya na daina sawa juna haraji mai yawan gaske a kan kayayyakin da suke cinikayya a tsakanin su.

Wannan yana zuwa kwana daya bayan da aka cimma yarjejeniyar data tanadi kasar ta China ta kara dayen kayayyaki a Amurka a kan farashi mai rahusa domin rage gibin cinikayya da China.

Sakataren Baitulmalin Amurka Steben Mnuchin ya fada wa gidan talabijin na Fod cewa kasashen biyu masu karfin arziki sun samu ci gaba sosai a tattaunawar su.

Yace yanzu haka sun amince a kan jadawalin daidaitawa a kan batutuwa da suka tsara.

Kanfanin dillacin labarai na China Dinhua ya ambato mataimakin Prime minister Liu He wanda shi ne ya jagoranci tawagar ta China a tattaunawar da suka yi da Amurka a satin da ya gabata yana cewa ba shakka kasashen biyu sun cimma matsaya a kan ba zasu sake tada jijiyar wuya ba game da harkokin kasuwanci, kuma zasu dakatar da batun haraji tsakanin su a halin yanzu

 

Exit mobile version