Rabiu Ali Indabawa" />

Amurka Da Koriya Ta Arewa Sun Sasanta, In ji Trump

a a ci gaba da taron kolin da aka shirya yi tsakanin Donald Trump da Kim Jong-un a Singapore ranar 12 ga watan Yuni kwanaki kadan bayan shugaban na Amurka ya soke shi.

Mista Trump ne ya sanar da haka bayan wata ganawa da ya yi da wani babban jakadan Koriya ta Arewa a Fadar White House.

Jakadan, Janar Kom Yong-chol ya mika ma Shugaba Trump wata wasika hannu da hannu daga Shugaba Kim Jon-un na Koriya ta Arewa.

Mista Trump ya ce wasikar mai jan hankali ce, amma daga baya ya ce bai riga ya karanta ta ba.

Ya kuma ce batun yadda aka kare yakin Koriya na cikin batutuwan da za a tattauna akan su a taron kolin na Singapore.

An tsayar da yakin Koriya wanda aka yi daga 1950-1953 ne ta hanyar sulhu, ba ta hanyar kulla yarjejeniya ba.

 

 

Exit mobile version