Amurka Na Binciken Kashe Sojojinta Huɗu A Nijer

Sakataren tsaron Amurka Jim Mattis ya ce rundunar soja na binciken mutuwar sojojin Amurka huɗu a Nijer da suka mutu a farkon wannan wata a hannun mayakan jihadin Islama.

Yayin da ake dawo wa da gawar ɗaya daga cikin sojojin a jiharsa ta Florida a wannan mako, Mattis ya ce rundunar za ta fidda sabuwar sanarwa da zarar ta samu bayanai a cikin lokaci.

Ya ce ana bincike a kan rashi da muka yi na dakarunmu. Mu a ma’aikatar tsaron muna son mu san abin da muke faɗi kafin mu bayyanar da su, kuma a wannan lokaci ba mu da cikakken bayanai a kan wannan batu. Zamu fitar da bayanai cikin gaggawa kamar yadda za su shigo mana, saboda muna alfahari da dakarunmu. Kamar yadda kuka sani, muna gudanar da bincike duk lokacin da aka kashe mana sojoji.

An kashe sojojin ne a farkon wannan wata a wani kwantan ɓauna da mayaƙan jihadin Isama suka yi wa dakarun Amurka da na Nijer a wani faɗda da ya yi sanadiyar kashe sojojin Nijer guda huɗu.

Sanata John McCain mai yawan sukar lamirin shugaba Trump ya yi barazanar shigar neman izinin sammaci na ƙarin bayani a kan wannan hari.

Exit mobile version