Fa'iza Mustapha Ta CRI" />

Amurka Na Bukatar Huawei, In ji Catherine Chen

Jaridar New York Times ta Amurka, ta wallafa wata mukala a jiya, wadda Catherine Chen, mataimakiyar shugabar kamfanin fasaha ta Huawei na kasar Sin ta rubuta, tana mai cewa, Amurka na bukatar kamfanin Huawei. Ta ce haramcin kamfanin Huawei a Amurka, ba kirkire-kirkire kadai zai rage ba, har ma da rage takara da kara farashin kayayyaki da yi wa Amurkawa da harkokin kasuwanci tarnaki daga samun fasahar sadarwa mafi inganci a duniya. Haka zalika ba zai tabbatar da tsaro ga tsarin sadarwar zamani na Amurkar ba.
A cikin mukalar mai taken “America needs Huawei” wato “Amurka na bukatar Hauwei”, Catherine Chen, ta ce umarnin da shugaba Donald Trump ya rattabawa hannu a ranar Laraba, ya shimfida tubalin haramta sayar da kayayyakin Huawei a Amurka ta hanyar ayyana dokar ta baci. Baya ga haka, umarnin sakataren harkokin cinikayyar kasar, Willbur Ross ya fara aiki a jiyan, wanda zai hana kamfanin Huawei, kamfanin dake kan gaba a duniya a fannin samar da kayayyakin fasahar sadarwa, sayen kayyayakin fasaha daga Amurka ba tare da amincewar gwamnatin kasar ba.
Mukalar ta ce, wannan haramcin zai illa a fannin hada-hadar kudi, ga dubban Amurkawa dake aiki da kamfanonin dake huldar kasuwanci da Huawei, wanda ke sayen kayayyaki da hidimomi da darajarsu ta kai sama da dala biliyan 11 daga kamfanonin Amurka a kowacce shekara. Kana, haramci kan Huawei, zai kawar da dubban ayyukan yi a Amurka. Ta ce la’akari da yadda ake amfani da kayayyakin kamfanin dake dauke da gomman tsarukan sadarwa na 4G a sassa daban daban na kasar, ciki har da yankunan karkara, haramcin zai tilastawa masu samar da waya a Amurka, kashe ‘yan kudadensu wajen maye gurbin kayayyakin Huawei da masu tsada da abokan takararsu ke samarwa.
Abu mafi muhimmanci a cewar mukalar shi ne, haramcin zai gaza cimma burinsa na karawa tsarukan sadarwar zamani tsaro. Ta ce tsaron tsarin sadarwar hakki ne na masu samarwa da sayar da kayayyakin da masu hidimar samar da tsarin sadarwa, wajen hada hannu cikin adalci da tabbaci, don gudanar da aikin takaita samun barazana. Kuma Huawei ta sha bayyana cewa, ba ta za amince da duk wani yunkuri na kai hari ko leken asirin abokan huldarta ba.
Baya ga haka, ware Huawei kadai saboda hedkwatarta a kasar Sin babu ma’ana, saboda kamfanonin sadarwa kamar Nokia da Ericsson su ma kamfanoni ne dake ayyuka irin na Huawei, kuma suna amfani da kayayyakin da aka kera a kasar Sin, wanda ya mamaye mafi yawan kayayyakin sadarwa da intanet da a yanzu ake amfani da su a Amurka. Ta ce ware kamfani guda, ko kuma dukkan kamfanonin daga kasa guda, ba zai yi komai wajen takaita barazanar dake tattare safarar kayayyakin sadarwa a duniya ba, kuma zai zage takara tsakanin kamfanoni, wanda a karshe, zai kara farashin kayayyaki.
Har ila yau, mukalar ta ce idan fadar White House da ma’aikatar cinikayyar Amurka na son kare tsarin sadarwar Amurka, ba mayar da hankali kan haramta kamfani guda ya kamata su yi ba, kamata ya yi su samar da ingantacciyyar dabarar kula da za ta dogara kan ayyuka mafi kyau, irin dabarar ce ma’aikatar tsaron harkokin cikin gidan kasar ta gabatar a bara.
A karshe, mukalar ta ce, yunkurin dakatar da wani kamfani, bare ma Huawei, jagora tsakanin takwarorinta, zai raunana takara da jinkirta amfani da fasahar 5G da rage kirkire-kirkire da yi wa abokan hulda Amurkawa da ‘yan kasuwa tarnaki daga samun fasahar sadarwa mafi inganci a duniya. Kamata ya yi, gwamnatin Trump ta dakatar da yunkurinta, a maimakon haka, ta samar da sahihin tsarin da zai tsare dukkan sassan tsarin sadarwar Amurka. (Fa’iza Mustapha

Exit mobile version