Amurka Na Shirin Fara Zafaffiyar Muhawara Kan Bakin Haure

Majalisar Dattawan Amurka na shirin fara wata shu’umar muhawara kan bakin haure daga ranar Litini. Muhawarar za ta kasance wata iriya, saboda za a fara ta ne ba tare da ainihin takardar kuduri ba.

Shugaban Masu rinjaye na Majalisar Dattawa Mitch McConnell ya ce za a bude muhawarar ce da wata takardar kudurin doka wadda babu batun bakin haure ciki. Daga baya sai ‘yan Majalisar su bukaci a yi gyara ma takardar.

A cewar McConnell gyarar da za a yi za ta tabbatar da adalci a yayin muhawarar.

‘Yan Majalisar za su tattauna kan kan makomar wasu matasan bakin haure da ke zama karkashin wani shirin da ke kare su daga kora mai suna DACA a takaice. Za kuma su tattauna kan batun gina Katanga a kan iyakar Amurka da Medico, da tsarin shigowa Amurka ta hanyar canki-canki, da tsarin shigowa Amurka ta hanyar gayyatar daga wani dangi da dai sauran batutuwa.

 

Exit mobile version