Wasu manyan jami’an Amurka guda biyu sun ce akwai yiwuwar Korea ta Arewa ta iya kawo harin makaman Nukiliya akan Amurka nan da wasu ‘yan watanni masu zuwa.
A jiya Alhamis, Darektan hukumar leken asirin kasar ta CIA, Mike Pompeo ya faɗawa a wani taro a nan Washington cewa “yana cikin matukar damuwa” kan yadda Korea ta Arewa ke ƙara zafafa barazanarta da kuma yiwuwarta haifar da gwagwarmayar neman mallakar makaman Nukiliya a tsakanin ƙasashen da ke yankin gabashin Asiya.
“Ya kamata mu riƙa ɗauka tamkar sun cimma wannan buri na su ne,” in ji Pompeo a lokacin da aka tambaye shi kan yiwuwar Pyongyang ta kawo hari akan wasu muhimman wurare a cikin Amurka.
“Tuni sun riga sun yi nisa wajen cimma wannan burin, yanzu an kai wurin tunanin ta yaya za a iya ja musu burki?”